Nasara: Yan bindiga da Yawa Sun Baƙunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Dirar Musu a Jihar Arewa

Nasara: Yan bindiga da Yawa Sun Baƙunci Lahira Yayin da Sojoji Suka Dirar Musu a Jihar Arewa

  • Sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna
  • Bayanai sun nuna dakarun sojin sun hallaka ƴan bindiga huɗu a musayar wutar kuma sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su
  • Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce sun samu wannan nasara ne a ranakun Talata da Laraba a wannan makon da muke ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda guda hudu a wani samame da suka saba kai wa a yankin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sashi na ɗaya ta hukumar sojin kasa a Najeriya, Laftanar Kanar Ibrahim Musa ya fitar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ga takansu yayin da sojoji suka ceto mata 18 a jihar APC, gwamnan arewa ya basu kuɗi

Dakarun soji sun samu nasara a Kaduna.
Sojoji Sun Murkushe Yan Ta'adda Hudu, Sun Ceto Mutum 11 a Jihar Kaduna Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Channels tv ta ce yayin wani sintiri cikin shirin ko ta kwana ranar Talata 6 ga watan Fabrairu, 2024 a Birnin Gwari, dakarun sojin suka yi gumurzu da ƴan bindigan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musa ya bayyana cewa yayin wannan artabu ne dakarun sojin suka yi nasarar tura ƴan bindiga 4 barzahu, sauran kuma suka ari na kare ɗauke da raunukan harbi.

Ya kuma ƙara da cewa sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda uku, mujallun AK-47 guda bakwai da kuma babura biyu daga hannun ‘yan ta’addan.

Sojoji sun ceto mutum 11 harda jariri

Bayan haka, sojojin runduna ta daya da aka tura garin Birnin Gwari sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su ciki har da wani jariri ɗan wata tara a kauyen Kwaga a lokacin da suka yi arangama da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Katsina

Kakakin rundunar ya bayyana cewa an ceto mutanen ne tranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, bayan da sojojin suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar.

Rundunar ta bayyana sunayen mutanen da aka ceto da suka hada da Zakari Galadima, Ishaku Galadima, Habibu Illaysu, Nuzuli Ibrahim, Ramatu Aliyu da Ubaida Mubarak.

Sauran sune Zaliha Mubarak, Umma Haruna, Khairatu Salisu, Rahamatu Usman da kuma Rakiyia Yahaya, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

A cewarsa, an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu daga kauyensu da ke Masuku a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Soji sun ceto mutum 18 a Katsina

A wani rahoton na daban Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da wasu mata 18 da aka yi garkuwa da su daga hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.

Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Raɗɗa ta bai wa kowace mace daga ciki kyautar N100,000 domin su kama sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262