"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimmin Saƙo Ga Ƴan Najeriya
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da fatan alkhairi a tunani da lafuzan bakinsu a kullun
- Ya bayyana hakan ne a bayyanarsa na farko tun bayan da ya dawo daga hutun makonni biyu da ya je a birnin Paris, Faransa
- Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan kasar da su yi koyi da 'yan wasan Super Eagles, da suka kyautata zato da yarda da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci'yan Najeriya da su dunga fatan alkhairi kan kasar, yana mai cewa irin haka zai bada damar samun ci gaba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da gidaje 3,112 daga cikin shirinsa na sabonta fatan birane a babban birnin tarayya.
Tinubu, wanda ya bayyana bainar jama'a karo na farko tun bayan dawowarsa dag hutun makonni biyu a Paris, Faransa ya bukaci 'yan kasar da su kyautata zato da magana mai kyau kan kasar duk da kalubalen da ake fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga daga garin Minna
Zanga-zangar da aka yi a baya bayan nan a Minna, Kano da Ondo ya nuna irin wahalar da ake sha saboda tsadar rayuwa.
A Minna, mata sun toshe hanyar Minna zuwa Bida, suna neman gwamnati ta dauki mataki don magance matsalar yunwa.
Jami'an tsaro sun yi yunkurin tarwatsa jama'ar da barkonon tsohuwa, lamarin da ya kai ga kama wasu.
Tinubu ya magantu kan muhimmancin fadin alkhairi
Tinubu, da yake jawabi a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, ya karfafawa 'yan Najeriya gwiwa kan su mayar da hankali wajen makomarsu maimakon tsayawa kan baya.
Ya jaddada cewar suna da kasa da ke fifita jin dadin al'ummarta.
Ya kuma nuna jajircewarsa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, rahoton Punch.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan kasar da su yi koyi da 'yan wasan Super Eagles, da suka kyautata zato da yarda da kai wanda ya kai su ga yin nasara a wasan kusa da karshe.
Yan Najeriya miliyan 88.4 na rayuwar talauci, FG
Mista Temitope Fadeshemi, sakataren din-din-din na ma'aikatar noma da tsaron abinci, ya bayyana cewa mutane miliyan 88.4 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci a Najeriya.
Fadeshemi ya yi magana ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, a Kaduna yayin rabon kayan amfanin gona da kayan tallafi ga kananan manoma
Asali: Legit.ng