Babban Labari: Tinubu Ya Bada Umarnin Fito da Metric Tan 102, 000 na Masara da Shinkafa

Babban Labari: Tinubu Ya Bada Umarnin Fito da Metric Tan 102, 000 na Masara da Shinkafa

  • A yammacin Alhamis, 8 ga watan Fubrairu, 2023, gwamnatin tarayya ta bada umarnin fito da kayan abinci.
  • Gwamnatin tarayya ta bada sanarwar nan ne ta bakin Alhaji Mohammed Idris, Tribune ta kawo labarin a dazu.
  • Mohammed Idris wanda shi ne Ministan labarai da wayar da kan jama’a ya ce halin da aka shiga ya jawo hakan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan ya amsa tambaya daga wajen manema labarai bayan zaman kwamitin da shugaban kasa ya kafa.

Mai girma Bola Tinubu ya samar da wani kwamiti na musamman da aka ba alhakin magance matsalar kayan abinci.

Masara da Shinkafa
Bola Tinubu ya ce a saki abinci Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abinci: Tinubu ya ce ayi duk abin da za a yi

A bayanin da ya yi a Aso Villa, Ministan ya ce shugaban kasa ya bukaci ayi duk yadda za ayi domin a samu abinci.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta ce shugaba Bola Tinubu ya nuna za a iya shigo da abinci daga ketare idan an samu gibi a noman gida.

Idan bukatar shigo da abincin ta kama, ministan ya shaida cewa za a bi duk wata hanya da za ta magance yunwa.

Kwamitin magance matsalar abinci

Business Day ta ce an dauki matakin ne bayan kwamitin nan ya shafe kwanaki uku a jere yana zama a birnin Abuja.

Wahalar rayuwa da zanga-zanga da aka fara ya jawo gwamnatin Tinubu ta gyara zama a sharewa talaka hawaye.

Gwamnati ta ce a guji boye abinci

A jiya aka ji labari Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya yi kwanaki a Faransa.

Gwamnatin tarayya ta ja-kunnen masu boye abinci, tayi kira ga jama’a su nuna kishin kasa a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

A na ta bangaren, gwamnatin Najeriya za ta dage wajen ganin an samar da isasshen abinci ta hanyar noma a gida.

Jama'a za su samu samu abinci?

Amma Dr. Abubakar Sani Abdullahi wanda masani ne a harkar samar da abinci yana da shakku a game da umarnin.

A wani bayani da ya yi wa Legit, ya nuna da kamar wahala hakar ta cin ma ruwa domin babu abincin da ake tunani.

Idan za a duba rumbunan kasar, yana ganin ba za a samu kayan abincin kirki ba, a karshe sai dai a shiga kasuwanni.

Muddin gwamnati ta shiga kasuwa domin sayen hatsi, masanin yana ganin farashin masara da shinkafa zai kara tashi.

Yunwa: Abba zai zauna da Tinubu

Ana da labarin cewa Gwamnan Kano yana neman yadda farashin kaya da abinci za su sauko musamman a jiharsa.

Mai girma Abba Kabir Yusuf zai hadu da Bola Tinubu kuma zai yi rabon abinci a duka kananan hukumomin da ke Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng