An Shiga Rudani Kan Batun Mutuwar Babban Basarake a Najeriya, An Fadi Gaskiyar Abin da Ya Same Shi
- Fadar mai martaba Asagba na Asaba ta fito ta yi magana kan batun mutuwar basaraken da aka yi ta yaɗawa
- Fadar ta bayyana cewa basaraken wanda yake dab da cika shekara 100 a duniya yana nan a raye da ransa bai mutu
- Sakataren fadar wanda ya musanta batun mutiwar basaraken, ya bayyana cewa mai martaba sarkin an kwantar da shi ne akwai a asibiti
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - An samu tashin hankali game da mutuwar Asagba na Asaba, Obi Chike Edozien.
Sai dai fadar a ranar Alhamis, ta ce basaraken gargajiyar yana kwance a asibiti ne kawai bai mutu ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Sakataren fadar, Ogbueshi Ndili ya bayyana haka lokacin da aka tuntuɓe shi ta wayar tarho.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mai Martaba Sarki yana kwance a asibiti ne kawai. Idan mutuwa ta riske shi, za mu sanar."
Hakazalika, da aka tuntubi ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Oshimili ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Bridget Anyafulu, kan wannan jita-jitar, sai ya kada baki ya ce:
“Ban san komai ba game da hakan.”
An yi ta yaɗa jita-jita da sanyin safiyar ranar Alhamis cewa, sarkin mai shekara 99 wanda zai cika shekara 100 a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara ya rasu, lamarin da ya haifar da fargaba a Asaba babban birnin jihar.
Jigon APC ya yanke jiki ya mutu
Wani jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ɗan majalisar wakjilai, wanda ya wakilci mazabar Ika ta jihar Delta a majalisar tarayya, Cairo Ojougboh, ya yi bankwana da duniya.
Ojougboh, wanda ya shahara saboda rashin tsoron fitowa ya yi magana ya rasu ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, yayin da yake kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON 2023.
Mataimakin Bursar Ya Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin Bursar na jami’ar jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a daren Laraba.
Marigayin ya rasu ne a lokacin da yake kallon wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.
Asali: Legit.ng