Mutane Miliyan 88.4 Ke Rayuwa Cikin Matsanancin Talauci a Najeriya, In ji Gwamnati

Mutane Miliyan 88.4 Ke Rayuwa Cikin Matsanancin Talauci a Najeriya, In ji Gwamnati

  • Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan yawan mutanen dake rayuwa cikin kangin talauci a kasa
  • Sakataren din-din-din na ma'aikatar noma, Temitope Fadeshemi ya ce mutane miliyan 88.4 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci a kasar
  • Sai dai kuma, ya ce akwai wasu tsare-tsare da gwamnatin Bola Tinubu ke yi don fitar da al'umma daga kangin talauci

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mista Temitope Fadeshemi, sakataren din-din-din na ma'aikatar noma da tsaron abinci, ya bayyana cewa mutane miliyan 88.4 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci a Najeriya.

Fadeshemi ya yi magana ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, a Kaduna yayin rabon kayan amfanin gona da kayan tallafi ga kananan manoma 250, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame malamin addini da matarsa saboda babban laifi 1 da suka aikata

Mutane miliyan 88.8 na rayuwa cikin talauci a Najeriya
Mutane Miliyan 88.4 Ke Rayuwa Cikin Matsanancin Talauci a Najeriya, In ji Gwamnati Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewaya ruwaito cewa, Bashir Abdulkadir, daraktan sashen ayyuka na ma’aikatar ne ya wakilce shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FG ta bai wa kananan manoma tallafi

An kuma rahoto cewa an bai wa manoman tallafi ne a karkashin shirin rage radadin talauci tare da bunkasar tattalin arziki (NPRGS).

Ya ce:

“Matsalar talauci a Najeriya yana da ban tsoro. Kimanin mutane miliyan 88.4 a Najeriya na rayuwa cikin matsanancin talauci.
"Adadin mazan da ke rayuwa a kasa da dalar Amurka 1.90 a kullun a kasar ya kai kusan miliyan 44.7, yayin da adadin mata ya kai miliyan 43.7.
“Gaba daya, kaso 12.9 cikin dari na al’ummar duniya daje rayuwa cikin matsanancin talauci an samu su a ne Najeriya a shekarar 2022.
"Wannan shine dalilin da ya sa gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tarayya tare da hadin gwiwar FMAFS ke kokarin rage radadin talauci a fadin kasar."

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya fallasa fastoci masu shirya mu'ujizar karya, ya fadi yadda suke yi

A cewar Fadeshemi, taron ya nuna gagarumin ci gaba a kokarin gwamnatin tarayya na bunkasa rayuwar kananan manoma da kuma bunkasa ayyukan noma mai dorewa, rahoton Osun Defender.

Fadeshemi ya ce shirin ba zuba jar ne kawai a harkar noma ba; face harda zuba jari a makomar al'umma.

Jigon APC ya roki 'yan Najeriya

A wani labarin, jigon jam'iyyar APC, Dr Olamide Ohunyeye, ya roki 'yan Najeriya a kan su kara hakuri da Shugaban kasa Bola Tinubu yayin da ake tsaka da fama da tsadar rayuwa a kasar.

Ohunyeye ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya bayyana a shirin "Situation Room" na wani gidan rediyo mai zaman kansa, Fresh FM a Akure, babban birnin jihar Ondo, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng