Babban Malamin Addini Ya Fallasa Fastoci Masu Shirya Mu'ujizar Karya, Ya Fadi Yadda Suke Yi
- Fasto Mbaka ya jawo cece-kuce a yanar gizo yayin da ya yi ƙarin haske game da wasu fastocin Najeriya
- A cewar Mbaka, wasu da ake kira fastoci da ake girmamawa suna zuwa cocinsa suna amfani da wanna damar, suna yaudarar mutane
- Sai dai, babban faston ya buƙace su da su daina irin wannan aika-aikar domin sam ba ta dace ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Fasto Ejike Mbaka, shugaban cocin Adoration Ministry, Enugu, Najeriya (AMEN), ya yi iƙirarin cewa yawancin fastocin Najeriya suna bayar da bayanan ƙarya da yin mu'ujizar ƙarya domin samun kuɗi da ɗaukaka.
Babban limamin cocin Katolikan ya bayyana hakan a cocin da ke birnin Enugu, cikin ƴan kwanakin nan.
Alamu sun nuna cewa an gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, 2024 inda wani faifan bidiyo ya nuna malamin yana bayyana hakan wanda aka ɗora a shafukan Facebook da YouTube na cocin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar PremiumTimes, faifan bidiyon ya ci gaba da janyo cece-kuce a faɗin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, yankin da ke da yawan mabiya addinin Kirista.
Mbaka ya soki yadda ake amfani da saƙonnin ubangiji don neman kuɗi, inda ya yi masa laƙabi da "haƙar kuɗi."
Mbaka ya jawo cece-kuce inda ya ce wasu fastocin sukan ziyarci cocinsa, su ɗauki hoto tare da shi, sannan su yi amfani da hoton wajen buɗe coci-coci da yaudarar mutane.
Wanene Ebuka Obi?
Bayan faifan bidiyo ya fara yaɗuwa, mutane da yawa sun nuna cewa tabbas malamin yana magana ne akan wani mashahurin fasto mai suna Ebuka Obi.
Obi, wanda ya kafa cocin Zion Prayer Movement Outreach, ya kasance na hannun daman Mbaka, kafin ya kafa cocinsa a a shekarar 2009.
Sai dai, Mbaka ya fayyace cewa bai ambaci sunan kowa ba amma ya yi gargaɗi game da shirya mu'ujizar ƙarya.
Ku kalli bidiyon a nan:
EFCC Ta Cafke Babban Fasto
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta cafke wani babban fasto kan zargin damfarar mabiyansa.
Hukumar tana zargin Apostle Theophilus Oloche Ebonyi da damfarar mabiyansa N1.3bn na wani tallafi.
Asali: Legit.ng