Tsadar Rayuwa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Jihar Arewa, An Yi Wa Mataimakin Gwamna Ihu

Tsadar Rayuwa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Jihar Arewa, An Yi Wa Mataimakin Gwamna Ihu

  • Kwana biyu bayan abinda ya auku a Minna, sabuwar zanga-zanga ta kuma ɓallewa a Suleja duk a jihar Neja
  • Mata, maza da matasa sun toshe manyan tituna lamarin da ya jawo wa matafiya tsaiko na tsawon awanni yau Laraba
  • Duk wani yunkuri da ƴan sanda suka yi domin tarwatsa mutanen bai cimma nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Awanni 48 bayan zanga-zangar da aka yi a Minna, babban birnin jihar Neja, sabuwar zanga-zanga ta saƙe ɓallewa a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, gungun masu zanga-zanga sun mamaye tituna a garin Suleja da ke cikin jihar Neja yau Laraba.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Zanga zanga a Neja.
Tsadar rayuwa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Neja Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kawo karshen wannan tsadar rayuwa saboda suna cikin wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ɗaga alluna masu ɗauke da rubutu daban daban kamar, "Tinubu ka yi wani abu yanzu," "shugabanci shi ne inganta rayuwar al'umma," "Ƴan Najeriya na cikin ƙunci," da sauransu.

Mata sun fito zanga-zanga

Wasu gungun mata sun toshe titin Minna zuwa Bida a daidai shataletalen Kpakungu domin nuna bacin ransu kan tsadar kayan abinci.

Lamarin dai ya rutsa da dukkan matafiyan da ke kan hanyar zuwa manyan birane a kudu kamar jihar Legas, Ibadan, da sauransu na tsawon sa'o'i.

Daga baya dai matan sun hadu da maza da matasa, inda suka ci gaba da nuna fushinsu da kuma zargin gwamnatoci da yin kunnen uwar shegu da halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da suka kai farmaki kan jami'an tsaro a jihar Arewa, an kashe sojoji

Mahukunta sun yi kokarin rarrashinsu

Duk wani yunƙuri da mahukunta suka yi da nufin tarwatsa masu zanga-zangar kama daga harba barkonon tsohuwa da harbin da ƴan sanda suka yi a iska, duk bai sa sun ja da baya ba.

Mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba, ya je wurin domin rarrashin masu zanga-zangar amma duk da haka ba su saurare shi ba.

Maimakon haka ma sai suka yi wa tawagar gwamnatin ihu, suna masu nanata cewa sun gaji haka nan, rahotom Channels tv.

Jagorar matan da suka fantsama zanga-zangar, Aisha Jibrin, ta ce:

"Mun fito zanga-zanga ne sabida karuwar tsadar rayuwa, babu abinda gwamnati take yi, ya kamata gwamnati ta tausaya mana, wasun mu sun wayi gari ba su da abinda zasu ci."

Kudirin gyara dokar zabe ya kai karatu na biyu

A wani rahoton kuma Kudirin sake garambawul a kundin dokokin zaben Najeriya 2022 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a majalisar wakilan tarayya.

Majalisar ta amince da kudirin a zaman ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024 bayan ɗan majalisa daga jihar Delta ya gabatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262