Matsalar Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Aike da Saƙo Ga NSA da Wasu Ministoci 3
- Majalisar dattawa ta canza shawara bayan manyan hafsoshin tsaro sun bayyana a gabanta yau Laraba a Abuja
- Jim kaɗan bayan ta basu damar shiga zauren, majalisar ta ɗage zaman sauraron ƙarin haske daga bakinsu, kana ta aike da gayyata ga NSA da wasu ministoci
- Sanata Godswill Akpabio ya ce hafsoshin tsaron za su dawo ranar Talata a makon gobe lokacin da sauran waɗanda aka ƙara gayyata zasu hallara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya, ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, ta aike da saƙon gayyata ga mai bada shawara kan tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu.
Bayan NSA, majalisar ta kuma gayyaci ministan tsaro, Muhammad Badaru, da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, domin su bayyana gabanta ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, 2024.
Kamar yadda The Nation ta tattaro, majalisar ta gayyace su domin su mata ƙarin haske kan matsalar tsaron da ke ƙara ƙamari a faɗin sassan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran waɗanda sanatocin suka gayyata kan batun tsaro sun haɗa da shugaban hukumar tattara bayanan sirri (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, da ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Majalisar dattawa ta yi amai ta lashe
Tun da farko, majalisar dattawa ta gayyaci hafsoshin tsaro da suka haɗa da babban hafsan tsaron ƙasa, Christopher Musa da shugaban rundunar sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja.
Sai kuma shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, sufetan ƴan sanda da shugaban DSS.
Amma jim kaɗan bayan waɗannan jiga-jigai sun bayyana a gaban sanatoci ranar Laraba, majalisar ta lashe amanta, kana ta ɗage zaman sauraronsu zuwa gaba.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da ɗage tattaunawa da hafsoshin tsaro da kuma aika sabuwar gayyata ga su NSA.
Ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin suna son ministocin tsaro, shugaban NIA da ministan cikin gida su halarci zaman sanatoci da hafsoshin tsaro, rahoton Channels tv.
Daga nan majalisar ta sallami shugabannin tsaron ba tare da daukar wasu bayanai daga bakinsu ba, sannan ta umarce su da su sake bayyana a ranar Talatar makon gobe.
FG ta fara ɗaukar matakan saukakawa al'umma
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta shirya daƙile matsalrar hauhuwar farashin kayan abinci da ake fama da ita a ƙasar nan.
Gwamnatin ta shirya haɗa kai da manyan masu casa da ƴan kasuwa don karya farashin kayan abinci.
Asali: Legit.ng