Bayan An Fara Zanga-Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Abu 1 Karya Farashin Kayan Abinci a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta shirya daƙile matsalrar hauhuwar farashin kayan abinci da ake fama da ita a ƙasar nan
- Gwamnatin ta shirya haɗa kai da manyan masu casa da ƴan kasuwa don karya farashin kayan abinci
- Gwamnatin ta yi nuni da cewa akwai abinci a ƙasar nan kawai dai wu ɓata gari ne ke amfani da wannan damar don azurta kansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A jiya ne gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakile tashin farashin kayan abinci a ƙasar nan.
Gwamnatin ta umurci kwamitin shugaban ƙasa na musamman kan samar da abinci cikin gaggawa da ya gaggauta ɗaukar mataki, cewar rahoton jaridar The Nation.
Da take tabbatar wa ƴan Najeriya cewa babu ƙarancin abinci, gwamnati ta yi zargin cewa masu zagon ƙasa na yin amfani da faɗuwar darajar Naira don ƙara tsadar kayan abinci, rahoton Vanguard ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Bola Tinubu da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne suka kira taron bisa umarnin shugaban ƙasa.
Wane mataki FG za ta ɗauka?
Bayan taron, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris ya ce za a fitar da kayan abinci daga rumbunan ajiyar abinci na ƙasa domin karya farashin.
Idris ya yi bayanin cewa gwamnati za ta haɗa kai da manyan masu casa da ƴan kasuwa domin samar da kayan abinci cikin sauƙi.
A kalamansa:
"Abin da zan gaya wa ƴan Najeriya shi ne, shugaban ƙasa ya ba da umarnin cewa akwai buƙatar gwamnati ta shigo cikin lamarin domin daƙile wannan hauhawar farashin.
"Gwamnati ba za ta naɗe hannunta ba ta ga yadda ƴan Najeriya ke shan wahala wajen samun waɗannan kayan abincin ba.
"Yanzu wasu daga cikin waɗannan matakan za su haɗa da fito da abincin da ake da shi ajiye a rumbunan ajiya da ke faɗin ƙasar nan. Kun san cewa ma'aikatar noma tana da rumbunan ajiya. Za a bayar da su ga ƴan Najeriya.
"Abin da gwamnati ke lura da shi shi ne har yanzu akwai abinci a ƙasar nan. Wasu na cin gajiyar lamarin, musamman saboda tsadar kayayyaki da kuma faɗuwar darajar Naira da ya sa farashin waɗannan kayan abincin ya tashi.
An Yi Zanga-Zanga a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga kan tsardar rayuwa a jihar Neja.
Mutanen dai sun fito kan tituna don nunawa gwamnatin cewa tura na neman kai bango kan yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng