Gwamnan PDP Ya Shigar da Sabbin Tuhume-Tuhume Kan Fitaccen Malamin Musulunci a Gaban Kotu
- Gwamnatin Bauchi ta shigar da sabuwar ƙara da sabbin tuhume-tuhume kan Sheikh Abdul'aziz Dutsen-Tanshi a kotun majistire
- Lauyan malamin ya bayyana cewa wanda yake karewa ya gudu ya bar gida ne bayan jami'an tsaro sun yi yunkurin damke shi
- A wata takardar kotu da aka liƙa a gidan malamin, gwamnatin Kauran Bauchi ta zargi malamin da ɓatanci da kalaman tunzura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a gaban kotu.
Sheikh Abdul'aziz, babban limamin masallacin Jumu'a na Dutsen-Tanshi ya yaƙi Gwamna Bala Muhammed tare da goyon bayan APC a zaben 18 ga watan Maris, 2023.
Premium Times ta ruwaito lauyan Mista Abdulaziz, Ahmad Musa, na cewa malamin ya gudu ne bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki gidansa na Dutsen Tanshi ranar 24 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdul'aziz dai ya bar jihar Bauchi ne domin ya gujewa gallazawa da tsare shi da gwamnatin Bauchi ka iya yi ba bisa ka'ida ba, biyo bayan tuhume-tuhumen da ake yi masa na aikata batanci ga addini.
Gwamnatin Ƙauran Bauchi ta shigar da sabbin tuhuma
Ranar Litinin, gwamnatin jihar ta ofishin Akanta Janar kuma kwamishinan shari’a, Hassan El-Yakub, ta shigar sabbin tuhuma a kotun majistare kan Malamin.
Sabbbin tuhume-tuhumen sun zargi Sheikh Abdul'aziz da "Kalaman tunzura jama'a, cin mutunci ko kuma tada jijiyar wuya na addini."
An manna sanarwar sabuwar karar da aka shigar da Malam Abdul'aziz a gidansa da ke Dusten-Tanshi a cikin babban birnin Bauchi.
A takardar kotun, za a ci gaba da zaman shari'ar ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu, 2024. Malamin dai ya musanta aikata laifin.
Lauyan Malamin ya bayyana cewa sabbin tuhume-tuhumen iri ɗaya ne da waɗanda aka shigar a babbar kotun shari'a 1 ta Bauchi.
Za a ciyar da bayin Allah a watan Ramadan
A wani rahoton na daban Gwamnan Kebbi ya yi alkawarin ɗaukar masallaci daya a kowace karamar hukumar jihar domin ciyar da abinci kyauta a cikin watan Ramadan.
Gwamna Idris ya ce gwamnatinsa zata yi wannan aiki na ciyar da al'umma a watan Ramadan ne ba don komai ba sai don neman yardar Allah.
Asali: Legit.ng