Hukumomin Tsaro Sun Fadi Sabbin Bayanai Kan Sanatan Arewa da Ake Zargi da Daukar Nauyin Ta'ddanci

Hukumomin Tsaro Sun Fadi Sabbin Bayanai Kan Sanatan Arewa da Ake Zargi da Daukar Nauyin Ta'ddanci

  • Bayanai sun bayyana dangane da zargin da ake yiwa wani sanata daga yankin Arewa kan tallafawa ta'addanci
  • Manyan jami’an leƙen asirin dai sun ƙaryata wannan iƙirari, inda suka bayyana shi a matsayin mara tushe da nufin ɓata sunan Sanatan
  • Sai dai kuma hukumomin tsaro sun jaddada ƙin amincewarsu da duk wanda ke da hannu wajen tallafawa ayyukan ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Manyan jami’ai daga wasu hukumomin leƙen asiri sun bayyana yunƙurin da wasu da ba a san ko su wanene ba suke yi na tunzura Sanatoci daga yankin Arewa a majalisar dattawa ta 10 a kan jama’a.

Da suke magana da PRNigeria ba tare da faɗin sunayensu ba, waɗannan jami’an sun bayyana cewa manufar waɗannan mutane shi ne su haifar da rashin jituwa a tsakanin jami’an tsaron ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin matsi a Najeriya, Remi Tinubu ta fadi lokacin da sauki zai zo

An bankado shirin bata sunan sanatan Arewa
Hukumomin tsaro sun bankado shirin bata sunan sanatan Arewa Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Bayanin nasu ya fito ne a matsayin martani ga wata jarida da ke iƙirarin cewa jami'an tsaro sun sa ido kan wani fitaccen Sanatan Arewa bisa zarginsa da taka rawar gani wajen ayyukan ta’addanci, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya yi zargin cewa wani fitaccen sanata da ke riƙe da wani babban muƙami a kwamitin majalisar dattawa, an gano shi a matsayin mai goyon bayan ayyukan ta’addanci a yankin Arewa.

Abin da hukumomin tsaron ke cewa

Sai dai wani babban jami’in leƙen asirin da ya yi magana a boye ya yi tir da rahoton, inda ya bayyana cewa binciken da suka yi ya gano asalin labarin, inda ya bayyana shi a matsayin “ƙirƙirarre".

Jami’in ya ce:

"Bincikenmu ya gano waɗanda ke yaɗa wannan labari mara tushe a kafafen yaɗa labarai, a halin yanzu, hukumar tsaron mu ba ta tuhuma ko bincikar wani Sanata kan ɗaukar nauyin ta’addanci."

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari a Yobe, sun tafka gagarumar barna

A halin da ake ciki kuma, wani babban jami’in soja, wanda bai bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa sun gano mutumin da ke da hannu a rahoton da aka wallafa na neman ɓata sunan Sanatocin Arewa.

Jami'an Tsaro Sun Sa Ido Kan Sanatan Arewa

Tun da farko rahoto ya zo cewa hukumomin tsaro sun sa ido kan wani sanatan Arewa da ake zargi da ba ƴan ta'adda kariya.

Ana dai zargin sanatan ne da ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci a yankin Arewacin Najeriya mai fama da matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng