Muhimmin Abu 1 Ya Jawo Gwamnan APC Ya Garƙame Manyan Makaranru 2 a Jihar Arewa
- Wasu manyan makarantun gaba da sakandire na kuɗi sun shiga matsala a jihar Kebbi bisa rashin biyan haƙƙin gwamnati
- Gwamnatin Kebbi karkashin Gwamna Nasir Idris ta sanar da kulle makarantun guda biyu har sai sun biya kuɗaɗen da ake binsu
- Kwamishinan ilimin gaba da sakandire na jihar Kebbi ya ce gwamnati ba ta ƙullaci makarantun ba kuma suna biyan kuɗin za a buɗe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ta garƙame manyan makarantun gaba sakandire guda 2 na kuɗi a jihar.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo a rahoto, gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne sabida gazawar makarantun wajen biyan haƙƙin gwamnati.
Makarantun da matakin ya shafa sun haɗa da Lamido Umaru Mutube College of Advanced Studies and Health Sciences da ke Dakin-gari da kuma SAHAM College of Health Sciences and Technology, Zuru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan kula da harkokin ilimi a matakin manyan makarantu na jihar Kebbi, Isah Abubakar Tunga, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce makarantun biyu za su ci gaba da zama a kulle har sai sun biya kuɗin harajin shekaru biyu da gwamnati ke binsu.
Sanarwan dai na ɗauke da sa hannun daraktan ilimin manyan makarantu na jihar, Aliyu Shehu Jega.
Meyasa gwamnati ta dakatar da makarantun?
Ya ce hukumomin waɗan nan makarantu sun ki biyan gwamnati haƙƙokinta na tsawon shekaru biyu duk da tunatarwa da gargadin da ma’aikatar ilimi ta aike musu.
A kalamansa, kwamishinan ya ƙara da cewa:
"Ba mu da wata matsala da su, kawai dai mun dakatar da su daga aiki ne saboda sun gaza biyan harajin shekara-shekara ga gwamnati.
"Za mu sake buɗe su nan take da zaran sun biya gwamnati kuɗaɗen harajin da take binsu bashi."
Gwamnan Kebbi ya shirya rabon abinci da Azumi
A wani rahoton kuma Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya yi alkawarin ɗaukar masallaci daya a kowace karamar hukumar jihar domin ciyar da abinci kyauta a cikin watan Ramadan.
Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mutanen kananan hukumomin Arewa da Dandi, wadanda suka kai masa ziyarar godiya ranar Litinin.
Asali: Legit.ng