An Shiga Jimami Bayan Halaka Mutum 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Arewa

An Shiga Jimami Bayan Halaka Mutum 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Arewa

  • Wasu miyagu sun kai harin ta'addanci a wasu guda uku na ƙaramar hukumar Otukpo da ke jihar Benue
  • A yayin mummunan harin da aka kai a ƙauyukan guda uku an salwantar da rayukan aƙalla mutum 17
  • Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce sun binne gawarwakin mutum bakwai yayin da za su ci gaba da neman sauran

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Aƙalla mutum 17 ne suka rasa ransu a wani hari da aka kai kan wasu ƙauyuka uku a yankin Entekpa da ke gundumar Adoka a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

Al’ummar yankin sun bayyana ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Iwili, Umogidi da Opaha a yankin Entekpa da ke gundumar Adoka a ƙaramar hukumar Otukpo, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kai farmaki wurin taron murnar nasarar gwamnan PDP a Kotun Ƙoli, sun tafka ɓarna

An kashe mutum 17 a Plateau
An salwantar da rayukan mutum 17 a Plateau Hoto: Emmanuel Ter
Asali: Twitter

Alfred Oketa Omakwu, shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, ya ce an gano gawarwaki bakwai da rana a ranar Talata, tare da taimakon sojoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omakwu ya ce za a ci gaba da neman ragowar gawarwakin idan sojoji sun dawo.

Wasu daga cikin mutanen sun ɓace

Wani mazaunin yankin da aka fi sani da Adakole ya shaida wa jaridar ta wayar tarho cewa jimillar mutum 17 ne ake fargabar sun mutu yayin da aka binne mutum huɗu.

A kalamansa:

"Muna fargabar an kashe ƙarin mutane, kodayake an gano gawarwaki huɗu a daren ranar Litinin. Gaba ɗaya mutum 17 ne suka ɓace. Muna tsammanin duk an kashe su amma har yanzu muna ci gaba da nemansu a cikin daji."

Da aka tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba ta samu rahoto kan harin ba.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari a Yobe, sun tafka gagarumar barna

An Tsinci Gawar Wani Matashi a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsinci gawar wani matashi babu wassan jikinsa yashe a Bola a jihar Benue.

An dai tsinci gawar matashin ne hannayensa na ɗaure ta bayansa tare da rauni a jikinsa wanda ya nuna kamar faɗa ne na ƴan ƙungiyar asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng