Mata Sun Barke da Zanga-Zanga Saboda Mazansu Ba Su Kusantarsu Idan Dare Ya Yi, Sun Fadi Dalili

Mata Sun Barke da Zanga-Zanga Saboda Mazansu Ba Su Kusantarsu Idan Dare Ya Yi, Sun Fadi Dalili

  • Zanga-zanga ta barke a birnin Port Harcourt inda mata suka cika titunan kan rashin wutar lantarki a birnin
  • Shugabar matan da ke zanga-zangar ta ce ba su samun jin dadin aure da mazajensu saboda tsananin zafi
  • Da aka tuntubi mai magana da yawun kamfanin wutar na PHED, Livingstone Koko ya ce wannan matsala ce da ta shafi kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - An shiga wani irin yanayi bayan wasu mata sun fito zanga-zanga a yankin Diobu da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers.

Matan sun fito ne don nuna damuwa kan kamfanin samar da wutar lantarki na PHED da ke hanasu saduwa da mazajensu saboda zafi.

Kara karanta wannan

Ana son kifar da Tinubu, APC ta tona asirin wadanda suka dauki nauyin zanga-zanga a Kano da Neja

Mata sun fito zanga-zanga kan rashin kusantarsu da mazajensu ke yi
Mata Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Rashin Wutar Lantarki. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Mene dalilin zanga-zangar matan a yau?

Matan sun koka cewa saboda rashin wuta mazajen nasu ba su zuwa kusa dasu don raya sunna saboda tsananin zafi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matan sun fito zanga-zangar ce a yau Talata 6 ga watan Faburairu inda suka ce rashin wutar ya kara musu kuncin rayuwa.

An gano matan dauke da kwalaye da ke nuna rubutu kamar haka "Ba wuta, ba biyan kudi", "Zafin ya yi tsanani" da sauransu.

Sun kuma koka cewa harkokin kasuwancinsu na durkushewa bayan rashin iya adana kayan abinci saboda rashin wuta, cewar PM News.

Martanin shugabar matan da ke zanga-zanga

Shugabar matan, Maria Ike ta ce:

"Mu na son sanar da duniya halin da muke ciki a hannun PHED duk da yawan kudade da muke biya a wata.
"Ba ma iya samun damar jin dadi da mazajenmu na aure saboda rashin wuta ga shi kasuwancinsu na neman durkushewa.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Da aka tuntubi mai magana da yawun PHED, Livingstone Koko ya ce wannan matsala ce da ta shafi ko ina a fadin kasar, Punch ta tattaro.

Ya ce kamfanin PHED na iya kokarinsa don ganin ya inganta wutar lantarki a fadin jihar baki daya.

An yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Kun ji cewa zanga-zanga ta barke a birnin Minna da ke jihar Neja a Arewacin Najeriya.

Masu zanga-zangar sun koka kan yadda rayuwa ta yi tsada ba tare da daukar wani mataki daga gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.