Dakarun Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a FCT, Sun Cafke Wasu

Dakarun Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a FCT, Sun Cafke Wasu

  • Ƴan sanda sun cafke mutum 6 da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja
  • A wata sanarwa da rundunar ƴan sanda ta fitar, ta ce an kama waɗanda ake zargin a maɓoyarsu da ke wani otal a kauyen Bassa
  • Kwamishinan ƴan sandan Abuja ya ce rundunar ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kawar da miyagun laifuka a FCT

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dakarun ƴan sanda na sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane sun damƙe mutum shida da ake zargin masu garkuwa ne a birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ƴan sanda sun kama masu garkuwan, da suka kunshi maza huɗu da mata biyu yayin da suka kai wani samane mafakar su.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan buƙatar magoya bayan gwamnan PDP da ake zargi da ta'addanci

Yan sanda sun kama masu garkuwa a Abuja.
Dakarun Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a FCT, Sun Cafke Wasu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar ƴan sandan Abuja ta lissafa sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da, Buhari Muhammad (20), wanda jami'ai suka jima suna nema ruwa a jallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune, Muhammad Sabiu (20), Isah Abdullahi, Hamzat Musa (21), Fatima Abdullahi (22) da kuma Zuliat Yusuf (23).

Dakarun sun damke su ne a wurin da suke ɓuya a wani Otal da ke kauyen Bassa a birnin tarayya Abuja.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin ne suka yi garkuwa da wani mai suna Joshua Eze, mijin Blessing Eze, matar da ta ji raunin harsashi a lokacin sace mijinta.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana haka a wata sanarwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ƴan sanda sun kwato kayayyaki a hannunsu

Kakakin ƴan sandan ta ce an kwato kudi N345,000 da wasu kayayyaki masu daraja daga hannun waɗanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Asirin waɗanda suka kashe sarakuna biyu a Najeriya ya fara tonuwa, an kama mutum 13

A cewarta, tuni dai masu garkuwan da aka kama suka amsa laifinsu tare da bayanin yadda suke aikata laifin garkuwa lokuta da dama a Abuja.

A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sanda, Benneth C. Igweh, ya baiwa jama’a tabbacin cewa zasu kawar da miyagun laifuka a babban birnin tarayya Abuja.

Ƴan daba sun farmaki wurin taro

A wani rahoton kuma Wasu matasa sun farmaki wurin taron da aka shirya domin murnar nasarar Gwamna Fubara a kotun koli a Ahoada ta yamma.

Rahoto ya nuna cewa ƴan daban sun lalata kujeru da rumfunan da aka sa a wurin, sai dai daga baya an sasanta kuma taron ya gudana cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262