"Jama'a Na Shan Wahala" Gwamna Abba Na Kano Zai Gana da Tinubu Kan Muhimmin Abu 1 Tal
- Gwamna Abba ya sha alwashin zuwa wurin Bola Ahmed Tinubu kan matsi da yunwar da mutanen jihar Kano ke ciki
- Abba Kabir Yusuf ya faɗi haka ne yayin ganawarsa da ƴan kasuwa da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatinsa
- Ya roki ƴan kasuwar su guji ɓoye kayan abinci yayin da azumin watan Ramadana ke ƙara kusantowa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce zai je wurin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, domin sanar da shi halin matsin tattalin arziki da yunwa da al’ummar jihar ke fuskanta.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da ƴan kasuwa da masu ruwa da tsakin jihar Kano a gidan gwamnati ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Abba Kabir ya kara da cewa zai roƙi Shugaba Tinubu ya kawo ɗauki domin sauƙaƙawa talakalawa rayuwar ƙunci da yunwa da suke fama da ita a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Yusuf ya ce ana fama da wahala da yunwa a faɗin kasar nan amma shi zai yi magana kan batun Kano ne kaɗai a matsayinsa na shugaba.
Zan je na gana da Tinubu - Abba
A rahoton Daily Nigerian, Abba Gida-Gida ya ce:
"Ni da kaina zan je na roki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sa baki ya duba halin yunwa da ake fama da ita a jihar Kano, domin ceto al’umma daga matsananciyar wahala.
"Mun san cewa sauran sassan kasar nan ana fama da yunwa, amma za mu je ne a madadin jihar Kano, kasancewar nan ne mazabarmu."
Ya ce yadda hauhawar farashin kayayyaki ke karuwa da kayan abinci da sauran bukatu na yau da kullum ke tsada yana da matukar tayar da hankali.
Yadda za a kawo karshen lamarin
Bisa haka Gwamna Abba ya ce akwai buƙatar a haɗa hannu wuri ɗaya domin nemo hanyar warware matsalar cikin sauƙi.
“Muna rokon ku ’yan kasuwa ku daina ɓoye kayan abinci, don Allah ku fito da shi ku sayar wa jama’a domin dakile hauhawar kayan abinci, musamman a wannan lokaci da azumin watan Ramadan ya gabato."
Duk da sukar da ya sha daga Bashir Ahmed, tsohon hadimin Buhari, matakin da Abba ya ɗauka ya yi wa ƴan Kano da yawa daɗi.
Halin da ake ciki a Kano
Wata matar aure, Ummahani Sulaiman, ta gaya wa Legit Hausa cewa tsadar kayayaki ta yi yawa fiye da tunani, ya kamata shugaban ƙasa ya ɗauki mataki.
A cewar matar mai zama a Ɗorayi Ƙarama, Gwamna Abba ya yi tunani mai kyau na zuwa wurin shugaban ƙasa domin shi ne jagoran Kano kuma hakan ya nuna shi shugaba ne na gari.
"Bari na faɗa maka jiya na je cefanen kayan haɗa abinci, da naje yau kayan da aka bani ba su kai yawan na jiya ba, da na tambaya saboda duk kuɗi ɗaya na bada sai ce mun suka yi sun ƙara tashi.
"Ina zamu sa rayuwar mu, to a haka ma mu da dama tunda zamu siya wasu suna tashi ba su da abinda zasu ci, gwamnati ba ta tausayin mu, Allah ya kawo mana sauki kawai."
Haka nan wani malamin makaranta a Hotoro, Sanusi Isiyaku, ya ce idan ka siya abu yau, gobe ka koma zaka siya za a ce maka ya kara kuɗi.
Ya ce:
"Yanzu kana samun N50,000 a wata, ko mata ɗaya ba zata riƙe maka ba balle a ce ka tara iyali, yunwa ta fara addabar mutane. Na ji daɗi da gwamnan mu zai je Villa, Allah ya sa a samu mafita a ƙasa baki ɗaya."
Matar Tinubu ta gana da matan gwamnoni
A wani rahoton kuma Mai ɗakin shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Bola Tinubu, ta gana da matan gwamnonin jihohi 36 a birnin tarayya Abuja.
Wannan zama na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama matsin rayuwa da tsadar kayayyaki sakamakon karyewar darajar Naira.
Asali: Legit.ng