“Bana So Na Auri Wacce Bata San ‘Da Namiji Ba, Akwai ‘Daga Hankali”: Jarumin Fim Ya Magantu

“Bana So Na Auri Wacce Bata San ‘Da Namiji Ba, Akwai ‘Daga Hankali”: Jarumin Fim Ya Magantu

  • Jarumin Nollywood Baaj Adebule ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan yta bayyana matsayinsa kan macen da bata san 'da namiji ba
  • Yayin wata hira da aka yi da shi, jarumin fim din ya bayyana cewa ba zai so ya auri tsarkakkiyar mace ba
  • Da yake ci gaba da bayani, Baaj ya bayyana cewa zai kasance abu mai 'daga hankali idan mutum ya yi kokarin saninta 'diya mace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitaccen jarumin fina-finan Kudu, Baaj Adelabu ya magantu kan ra'ayinsa na rashin son macen da bata san 'da namiji ba.

Jarumin fim din, wanda ya bayyana a matsayin bako a shirin Pulse Hot Takes, ya magantu kan dalilin da yasa ya gwammaci kasancewa da matar da take ba tsarkakkiya ba.

Kara karanta wannan

Yadda masu garkuwa da mutane suka kashe shugaban makarantar Kaduna, ya bar mata 3 da yara 13

Jarumin fim ya ce baya son macen da bata san namiji ba
“Bana So Na Auri Wacce Bata San ‘Da Namiji Ba, Akwai ‘Daga Hankali”: Jarumin Fim Ya Magantu Hoto: @baajadebule
Asali: Instagram

A cewar Adebule, ya ce tsarin raba mace mai tsarki da budurcinta matsala ce da yake kallo a matsayin mai 'daga hankali. Ya kara da cewar ya kasance a matsayin a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake ci gaba da magana, jarumin ya kara da cewar mutane na yawan duba matar dake fuskartar lamarin amma ba namijin da shine zai yi aika-aikar ba.

Kalamansa:

"A'a...Saboda da fari, a fili wannan yana nufin cewa kai za ka kawar da budurcin, wanda abu ne da na taba fuskanta a baya kuma akwai 'daga hankali. Idan mutane suna tunaninsa.
"Macen kawai suke tunani, babu wanda ya taba tunanin namijin da abin da yake fuskanta, abu ne mai matukar ban tsoro."

Jama'a sun yi martani

soniaglitzy:

“Ku tambayi Israel abin da budurwa ta yi masa."

whitechief1:

"Wato kenan kuna so ku yi wa mata kamfen kan su jeru a lalata su ko?"

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

mz_lilianna:

"Kwastama ya ajiyewa 'yan gidan magajiya karin bayani."

@naomi_ville:

"Amsoshin da ke ƙarfafa lalata., kakadarta ace 'yar matashiyar yarinya ta ga wannan."

Uba ya aurawa malaminsa yaransa mata 2

A wani labarin kuma, mun ji cewa ana zargin wani uba mai suna, Umar Abubakar, da aurawa wani malaminsa, Gausu Mustapha, yaransa mata su biyu a lokaci guda a jihar Doso dake kasar Nijar.

Uwar rikon yaran ne ta yi karar Abubakar gaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, inda ta nemi a yi mata iyaka da mahaifin yaran wanda ke kokarin kwashe su don mayar da su hannun malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng