An Yi Rashi: Babban Shugaban Kasa a Nahiyar Afirika Ya Rasu, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasar Namibia, Hage Geingob ya rasu a safiyar Lahadi yana da shekaru 82, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta tabbatar
- Mataimakin shugaban ƙasar, Nangolo Mbumba ne zai karbi ragamar mulkin ƙasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki nan da ƙarshen shekara
- Fadar shugaban ƙasar ba ta bayyana musabbabin mutuwar Geingob ba, amma ya tafi Amurka a ƙarshen watan da ya gabata don jinyar cutar daji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƙasar Namibia - Hage Geingob, shugaban ƙasar Namibiya, ya rasu yana da shekara 82 a duniya a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu.
Fadar shugaban ƙasar ta sanar a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na twitter, makonni bayan an gano cewa yana ɗauke da cutar daji.
Geingob ya zama shugaban ƙasar ne wacce ke Kudancin Afirika a shekarar 2015, a wannan shekarar ya bayyana yadda ya tsira daga cutar sanƙara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban ƙasar Nangolo Mbumba ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar na wucin gadi har zuwa lokacin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a ƙarshen shekara.
Sai dai sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na twitter ba ta bayyana musabbabin mutuwar Geingob ba.
Gwamnatin ƙasar ta ce shugaban ya tafi Amurka ne a ƙarshen watan da ya gabata domin yi masa magani na kwanaki biyu don maganin ciwon daji.
Wanene Hage Geingob?
An haife shi a shekara ta 1941. Ya kasance fitaccen ɗan siyasa kafin ƙasar Namibia ta samu ƴancin kai daga Afirika ta Kudu a shekarar 1990.
Geingob shi ne shugaban kwamitin da ya tsara kundin tsarin mulkin ƙasar kuma ya zama firaminista na farko a ranar 21 ga Maris, 1999 inda ya bar ofishin a shekara ta 2002.
A shekarar 2007, marigayi shugaban ƙasar ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar SWAPO, ƙungiyar da ya shiga a lokacin fafutukar neman ƴancin kan ƙasar a lokacin da ake kiran ƙasar da sunan South West Africa.
Tun bayan samun ƴancin kai, SWAPO ta ci gaba da rike madafun ikon ƙasar Namibia.
Matar Mahaifin Kashim Shettima Ta Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa matar mahaifin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta riga mu gidan gaskiya.
Hajja Hauwa Kormi ta rasu tana da shekara 69 a duniya bayan ta yi fama da jinyar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng