Kotu Ta Tura Wanda Gwamnan PDP Ya Ba Mukami Magarkama Saboda Babban Dalili 1 Tak
- Wata babbar kotun tarayya dake Osogbo ta aika Olalekan Oyeyemi, mamba a hukumar kula da wuraren shakatawa na Ile-Ife, jihar Osun magarkama
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ne ya ba Oyeyemi, wanda aka fi sani da Emir mukami a hukumar kula da wuraren shakatawar
- Kamun da tuhumar da ake masa ya samo asali ne daga zargin cewa Oyeyemi ya lakadawa wani mutum duka har sai da ya rasa inda yake a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Osogbo, jihar Osun - Babbar kotun tarayya dake Osogbo, jihar Osun, ta tura wani mamba a hukumar kula da wuraren shakatawa na Osun, Olalekan Oyeyemi, wanda aka fi sani da Emir, magarkamar Ile-Ife.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ne ya nada wanda ake zargin a hukumar kula da wuraren shakatawar a watan Janairun 2023, Osun Defender ta ruwaito.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta maka Oyeyemi a kotu, inda take tuhumarsa kan abubuwa 11.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da yasa aka kama Olalekan Oyeyemi
Jaridar Punch ta rahoto cewa sashin yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar 'yan sandan jihar Osun ne ya kama Oyeyemi a 2023 kan zargin yi wa wani mutum duka har ya rasa inda kansa yake.
An gurfanar da wanda ake zargin ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu. Sai dai kuma, lauyan Oyeyemi, Edmund Biriomoni, ya yi tsokaci kan batun shari’a kafin a karanta tuhumar da ake masa.
Lauyan ya ce ya shigar da kara na farko kan zargin kisan kai da ake yi wa wanda yake karewa.
'Dan sanda mai kara ya mayar da martani
Da yake martani, 'dan sanda mai gabatar da kara, Umar Usman, ya nemi kotu ta janye tuhumar farko da ake masa sannan ta maye shi da wani da aka gyara.
Daga bisani Usman ya bukaci kotun da ta amsa rokon wanda ake kara, bayan da ta amince da gyararriyar tuhumar da aka yi masa.
Da yake yanke hukunci kan lamarin, Mai shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel ya amince da janye karar tare da maye gurbinsa.
Daga nan sai ya tura wanda ake kara zuwa gidan gyaran hali na Ile-Ife sannan ya umurci Biriomoni da ya shigar da kara a hukumance domin kin amincewa da gyara tuhumar a madadin wanda yake karewa.
Mai shari’a Ayo-Emmanuel ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar Talata 5 ga watan Maris.
Gwamnan Oyo ya fadi dalilin tsige basarake
A wani labarin kuma, mun ji cewa kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya ce gwamnatin jihar Oyo ba za ta ɗaga ƙafa kan duk wani wanda ya saɓa wa doka ba, komai girmansa.
Oyelade na mayar da martani ne kan dakatarwar da gwamnatin jihar ta yi wa Onido na yankin Ido, Oba Gbolagade Muritala Babalola (Gbadewolu I), a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Punch.
Asali: Legit.ng