Gwamman PDP Ya Dakatar da Fitaccen Basarake a Jiharsa, Ya Faɗi Muhimmin Dalili
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya dakatar da basaraken yankin ƙaramar hukumar Ido, Oba Gbolagade Babalola (Gbadewolu I)
- Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, Olusegun Olayiwola ne ya sanar da haka ranar Jumu'a, 3 ga watan Fabrairu
- Ya ce mai girma gwamna ya yi amfani da ƙarfin ikon da doka ta ba shi ne wajen ɗaukar wannan matakin kan Onido na Ido
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da dakatar da basaraken garin Ido da ke karamar hukumar Ido a jihar, Oba Gbolagade Babalola (Gbadewolu I).
Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, Gwamna Makinde ya dakatar da shi daga kujerar sarautar yankin wacce ake kira da Onido na Ido.
Wannan matakin na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Olusegun Olayiwola.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya fitar da sanarwan dakatar da sarkin ne yau Jumu'a, 2 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Mista Olayiwola ya bayyana cewa Gwamna Makinde ya rattaɓa hannu kan matakin dakatar da basaraken tun ranar 1 ga watan Fabrairu, 2024.
Meyasa aka dakatar da basaraken?
Sai dai bai bayyana maƙasudin dakatar da basaraken ba amma an umarce shi da ya miƙa dukkan wasu takardu da kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga shugaban ƙaramar hukumar Ido.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Ina mai sanar da ku cewa mai girma gwamna, Seyi Makinde, bisa la'akari da karfin ikon da doka ta ba shi, ya amince da dakatar da Onido na Ido da ke yankin ƙaramar hukumar Ido a jihar Oyo."
Gwamnan ya kafa hujja da sakin layi na 1 da 2 a sashi na 26 da ke ƙunshe a kundin dokar masarautu Cap. 28 Vol I na jihar Oyo 2000 wajen dakatar da basaraken.
A shekarar 2018, Babalola ya samu sabani da korarren Baale Tajudeen Agura, wanda ya tabbatar da halaccinsa a matsayin Onido na Ido saboda nasabarsa ta gidan Agura.
Gwamnan jihar Ondo ya naɗa kwamishinoni
A wani rahoton kuma Gwamna Aiyedatiwa na jihar Ondo ya maida mutum hudu daga cikin kwamishinonin da ya kora daga aiki.
Hakan na kunshe ne a jerin sunayen sabbin kwamishinonin da gwamnan ya aike ga majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng