Ministan Tinubu Ya Bayyana Mugun Mawuyacin Hali da Za a Shiga Idan Ba a Cire Tallafi Ba
- Yajin da ake ci gaba da shan wahala bayan cire tallafin mai a Najeriya, Ministan Tinubu ya kare matakin da shugaban ya dauka
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu a Abuja
- Minstan ya ce da ba a cire tallafin mai din ba da a yanzu haka ba a san halin da kasar ke ciki ba na mawuyacin hali
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris ya kare matakin cire tallafin mai a kasar.
Minstan ya ce da ba a cire tallafin mai din ba da a yanzu haka ba a san halin da kasar ke ciki ba na mawuyacin hali.
Mene Ministan ke cewa kan tallafin mai?
Idris ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed ya ce dole ne Tinubu da mukarrabansa suka sake sauya akalar kasar musamman ta fannin tattalin arziki.
A cewarsa:
"Ya kamata 'yan Najeriya su gane cewa dole ta saka Tinubu da mukarrabansa suka sauya akalar kasar ta fannin tattalin arziki tun daga farko."
Babban dalilinsa na kare cire tallafin
Ya kara da cewa:
"Ku duba maganar tallafi dole sai ta tafi, dole ne kuma ya sani za a fuskanci wahalalun cire tallafin, tabbas.
"Ya san da wahalar da za a shiga amma dole ya cire saboda idan ba a cire ba wahalar za ta fi haka, idan ba haka ko ayyuka ba za a iya yi ba."
Ministan ya ce dole ne a samar da kudade da aka samu ta bangaren don ayyukan ci gaban kasa, cewar Daily Trust.
An bukaci Tinubu ya cireka tallafin wutar lantarki
Kun ji cewa Ministan Makaman a Najeriya, Adebayo Adelabu ya shawarci cire tallafin wutar lantarki a Najeriya.
Ministan ya ce hakan zai rage yawan basukan da kamfanin ke bin gwamnatin wanda ke hana samar da wutar ingantacciya a kasar.
Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Asali: Legit.ng