Shehu Sani Ya Yi Martani Ga Hasashen Fitaccen Malamin Addini Na Cewa Naira Za Ta Fi Dala Karfi
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya fada ma yan Najeriya abun da ya kamata su ce dangane da addu'ar Fasto Enoch Adeboye kan farfadowar darajar naira
- Sanata Sani ya ce bai kamata yan Najeriya su yi tsokaci kan hasashen cewa naira za ta fi dala karfi ba
- Ya bayar da shawarar cewa kamata ya yi yan Najeriya su ce amin kan hasashen cewa naira za ta dawo ta fi dalar Amurka karfi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani ga hasashen da Fasto Enoch Adejare Adeboya, shugaban cocin RCCG ya yi na cewa naira za ta dawo ta fi dala daraja.
Sani ya ce 'yan Najeriya basa bukatar yin tsokaci da muhawara game da yadda hasashen zai zama gaskiya.
Ya ce abin da ake bukatar mutane su yi shine ihun Amin ga hasashen da malamin addinin ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @ShehuSani, a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu.
Ya rubuta:
"Don Allah, kada ku yi martani kawai ku yi ihun Amin."
Yan Najeriya sun yi martani
@AGINAS:
"Wannan Naira tana da taurin kai. Ji fa ta ki yin biyayya ga malamin addini."
@FirstObidient
"Ayi hakuri yallabai, Naira ba za ta tashi da wuta ba."
@emmofie
"Kana gaggawa sanata na. Ka kwantar da hankalinka yanzu haka sun dukufa azumin kwanaki 50. Naira za ta koma $1"
@Good_citizins
"Naira tana juyawa ta daya bangaren, Watakila zaurance ya yi. Abubuwan ruhi haka suke sau da dama."
Wasu yan Najeriya na shirin zanga-zanga
A wani labarin, mun ji cewa wasu magoya bayan Peter Obi, sun gaji da yadda abubuwa su ke tafiya tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu mulki.
An samu wasu daga cikin mabiya ‘dan takaran na LP a zaben 2023 da suke ganin ya kamata a fara shirya zanga-zanga a kasar.
Prophet Switch ya yi amfani da shafin X inda ya yi kira ga ‘dan takaran shugaban kasar da ya jagoranci a shirya zanga-zanga.
Asali: Legit.ng