Bam da Ƴan Ta'adda Suka Dasa Ya Tashi da Bayin Allah a Jihar Arewa
- Wani bam da ake kyautata zaton ƴan ta'addan Boko Haram ne suka dasa shi ya salwantar da rayukan mutum 12 a jihar Borno
- Bam ɗin dai ya tashi ne lokacin da motar da ke ɗauke da mutanen ta taka shi a kan babbar hanyar da ke wajen ƙauyen Pulka
- Rahotanni sun yi nuni da cewa akwai mutum uku da suka samu munanan raunuka a sakamakon tashin bam ɗin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Aƙalla mutum 12 masu sana'ar yin itace ne aka kashe a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.
Mutanen sun rasa ransu ne a kusa da kan iyaka da Kamaru a lokacin da motarsu ta taka wata nakiya a yankin da mayakan Boko Haram ke kai hare-hare, cewar rahoton Vanguard.
Masu saran itacen na kan hanyarsu ta zuwa daji ne domin yin itace, sai motar da ke ɗauke da su ta taka wata nakiya da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram n suka dasa a kan babbar hanyar da ke wajen ƙauyen Pulka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu ƙungiyoyin da ke bayar da agaji a yankin sun fitar da rahoto kan aukuwar lamarin.
Wacce irin ɓarna bam ɗin ya yi?
Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta fitar da rahoton cewa:
"Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne… sun tayar da bama-bamai, sun kashe mutum 12 yayin da da dama suka jikkata a hanyar Pulka zuwa Gwoza."
A cewar ɗaya rahoton, wanda ya bayar da irin wannan adadin, wasu masu sana'ar yin itace mutum bakwai sun samu raunuka, inda uku daga cikinsu na cikin mawuyacin halin da sai da aka tafi da su zuwa Maiduguri domin ba su kulawa.
Jami’an tsaro ba su bayar da amsa ba lokacin da aka tuntuɓesu domin tabbatar da aukuwar lamarin.
An samu ƙaruwar fashewar nakiyoyi waɗanda ake dasawaa kan ayarin motocin fararen hula a baya-bayan a jihar Borno.
Bam Ya Tashi a Borno
A baya rahoto ya zo cewa wani bam ya tashi a ƙaramar hukumar Gubio ta jihar Borno inda ya halaka mutum shida.
Bam ɗin ya tashi ne bayan an yi kuskuren ajiyesa cikin kayan ƙarafa a wani gini da ba a kammala ba kusa da wata makarantar Tsangaya.
Asali: Legit.ng