Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Cikin Gida, Sun Yi Garkuwa da Ƴan Mata 2 a FCT Abuja
- Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun shiga har cikin gida, sun sace ƴan mata 2 ƴan uwan juna a birnin tarayya Abuja
- Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun yi yunkurin yafiya da ƴan uwa uku amma daga bisani suka sako namijin ya dawo
- Rundunar ƴan sanda reshen FCT Abuja ba ta ce komai ba kan wannan sabon harin wanda ya zo a daidai lokacin da tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƴan bindiga su shida sun kutsa kai da tsiya cikin wani gida a kauyen Guita da ke yankin Chikakore a Kubwa, karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.
Yayin harin, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu ƴan mata biyu ƴan uwan juna, waɗanda ba su zarce shekaru 16 da 14 a duniya ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro ‘yan bindigar sun tsere ne ta wani daji, wanda ya hada garin da kuma wani kauye da ke maƙota duk a yankin ƙaramar hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum 3 ƴan bindigan suka ɗauka da farko
Wani mazaunin garin wanda ba ya son a faɗi sunansa saboda tsoron shiga matsala, ya ce da farko maharan sun dauki ‘yan uwa uku, 'yan mata biyu da namiji daya.
Amma daga bisani suka turo yaron ya koma gida, kana suka tafi da yara matan guda biyu zuwa cikin daji.
A ruwayar Sahara Reporters, mutumin ya ce:
"Lokacin da ƴan bindigan suka zo, ba su yi harbi kamar yadda suka saba ba, sun kutsa cikin gidan ne kawai, da maigidan ya fahimta sai ya ruga ofishin ƴan banga, ya wuce gidan kwamanda.
"A sa'ilin da kwamandan ya kira wani ɗan banga suka nufi gidan mutumin, tuni maharan sun gama abinda suka yi niyya sun tafi."
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, bai yi nasara ba saboda kiran da aka yi mata ta wayar salula ba ta ɗaga ba har yanzu.
An faɗi asarar da aka tafka a rikicin Mangu
A wani rahoton kuma Shugaban matasan Mwaghavul ya bayyana adadin rayuka da dukiyoyin da aka rasa a rikicin da ya ɓarke a Mangu, jihar Filato makon jiya.
Kwamared Sunday Ɗankaka ya ce mutane 91 sun mutu, wasu 158 sun ji raunuka yayin da aka ƙona gidaje da wuraren ibada.
Asali: Legit.ng