Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Kama Gadan-Gadan a Wata Babbar Coci a Najeriya
- Gobara ta tashi gadan-gadan a wata babbar coci da ke karamar hukumar Ikeja a jihar Legas, a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu
- Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta tabbatar da faruwar lamarin tare da alakanta hakan da zafin rufin cocin
- Wani bidiyo ya nuna yadda wuta ke ci a rufin ginin cocin da kuma yadda jama'a suka yi dandazo suna jimamin lamarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ikeja, jihar Legas - Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta tashi a cocin Household of David da ke karamar hukumar Ikeja a jihar Legas.
Amodu Shakiri, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Legas, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Shakiri, ya ce tsananin zafin da rufin dakin taron cocin ya dauka ne ya yi sanadiyyar ruguzowar rufin, wanda ya haddasa gobarar tashi nan take, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ba da tabbacin cewa jami’an kashe gobara tare da sauran hukumomin da abin ya shafa suna gudanar da aiki tukuru don shawo kan gobarar.
The Punch ta wallafa bidiyon irin barnar da gobarar ta yi.
Asali: Legit.ng