Kungiyar NLC Ta Tona Sirrin Wasu Gwamnoni da Aka Sanya a Kwamitin Mafi Karancin Albashi

Kungiyar NLC Ta Tona Sirrin Wasu Gwamnoni da Aka Sanya a Kwamitin Mafi Karancin Albashi

  • Shugaban NLC na ƙasa ya soki wasu gwamnoni da aka sanya a kwamitin mafi ƙarancin albashi mai ƙunshe da mambobi 37
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin ranar Talata a fadar shugaban ƙasa
  • Kwamared Joe Ajaero ya ce mafi akasarin gwamnoni da aka sa a kwamitin ba su biyan mafi ƙarancin albashi a jihohinsu kamar yadda doka ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya ce galibin gwamnonin da aka sa a kwamitin mafi karancin albashi mai mambobi 37 ba su iya biyan ma'aikatan jihohinsu.

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima, ya rantsar da kwamitin wanda zai sake nazari kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya yaba kan bambanci 1 da Tinubu ya nuna tsakanin Peter Obi da Atiku

Shugaban NLC, Joe Ajaero.
NLC: Mafi yawan gwamnonin cikin kwamitin ƙarancin albashi ba su biya a jihohinsi Hoto: NLC
Asali: Twitter

Da yake kaddamar da kwamitin ranar Talata, Shettima ya ce an yi haka ne domin tabbatar da albashi mai tsoka ga ma'aikata da kuma biyayya ga dokar mafi ƙarancin albashi 2019.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ya bankado sirrin wasu gwamnoni da ke cikin kwamitin

Da yake jawabi ranar Talata a gidan Talabijin na Channels cikin shirin 'Siyasa a yau' shugaban NLC, Mista Ajaero ya ce:

"Mafi akasarin gwamnonin da ke cikin kwamitin mafi karancin albashi, su ne wadanda ba sa biyan mafi karancin albashi ko kuma suna biyan ta hanyar da ta saɓawa doka.
"Gwamnonin da ke biyan cikakken mafi ƙarancin albashi a jihohinsu ba su samu wakilci ba a kwamitin. Don haka ko ma wane dalili ne ya sa gwamnatin tarayya ta sa gwamnonin da ba su biya a kwamitin zai fasu."

Wane jihohi ne ba su biyan mafi ƙarancin albashi?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

Da aka nemi ya faɗi sunayen wasu jihohin da suka gaza aiwatar da mafi karancin albashi, Ajaero ya ce:

"Jiha kamar Zamfara, ban san ko nawa ake biya a Borno da Bauchi ba, akwai dokar mafi karancin albashi wanda ta ayyana ƙin biyan mafi ƙarancin albashi a matsayin babban laifi."

Majalisar wakilan tarayya ta yi kwaskwarima ga dokar mafi ƙarancin albashi ta 2017 inda ta tanadi sake nazari kan albashin ma'aikata duk bayan shekaru biyar.

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan dokar a shekarar 2019, ma'ana a 2024 za a sake duba mafi ƙarancin albashi, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Delta ya dakatar da kwamishina

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Delta ya dakatar da kwamishinan noma da albarkatun ƙasa, Omoun Perez, tare da wasu manyan jami'ai a ma'aikatarsa.

Sherrif Oborevwori ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin baiwa kwamitin binciken damar gudanar da aikinsu ba tare da samun tsaiko ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262