Majalisa Ta Dauki Muhimmin Mataki Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro a Jihar Arewa
- Majalisar wakilai ta tashi tsaye domin maganace rikicin da ke aukuwa a jihar Plateau wanda ya halaka mutane masu yawa
- Majalisar ta amince da kafa wani kwamiti wanda zai binciki musabbabin kai hare-haren na ta'addanci da ake yi a wasu ƙananan hukumomin jihar
- Kafa kwamitin dai ya biyo bayan wani ƙuduri da wasu ƴan majalisa biyu na jihar ta Plateau suka gabatar a zauren majalisar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta amince da kafa wani kwamiti da zai binciki musabbabin hare-haren ta’addancin da aka kai a ƙananan hukumomin Mangu, Bokkos, Barkin Ladi da Riyom na jihar Plateau.
Amincewar ta biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa Ishaya David Lalu da ɗan majalisa Dalyop Fom Chollom suka gabatar a zauren majalisar a ranar Talata, cewar rahoton Daily Trust.
Da suke gabatar da ƙudirin, ƴan majalisar sun ce an kai hari kan al’ummar ƙaramar hukumar Mangu a ranar 24 ga watan Janairu, 2024, inda aka kashe sama da mutane 50 yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ƙara da cewa:
"Sama da gidaje 1,000 da kadarori na biliyoyin nairori sun lalace gaba ɗaya inda mutane kusan 20,000 suka rasa matsugunansu inda suka koma sansanonin ƴan gudun hijira daban-daban a ciki da wajen yankin.
"Yawancin waɗanda suka samu raunuka daban-daban a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban na jihar.
"Hare-haren da ƴan ta’addan ke ci gaba da kaiwa a ƙaramar hukumar na buƙatar a gaggauta magance su."
Wane mataki majalisar ta ɗauka?
Majalisar ta buƙaci babban hafsan tsaron ƙasar da ya kafa rundunar haɗin gwiwa ta farar hula a jihar Plateau tare da umartar kwamitocin tsaro da bin doka da oda su tabbatar an yi hakan.
Ana sa ran za su riƙa ba majalisar rahoton mako-mako har sai an shawo kan matsalar rashin tsaron.
Jaridar Vanguard ta ce a zaman majalisar na ranar Talata, ta kuma buƙaci shugaban hukumar Kwastam ya bayyana a gabanta kan gaza bayyana bayanin shige da ficen kuɗin hukumar na shekara uku.
Ɗan Majalisa Ya Sharɓi Kuka Yayin Zaman Majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa kakakin majalisar wakilai ya kece da kuka ana tsaka da zaman majalisa.
Akin Rotimi ya kece da kuka ne yayin da ake gabatar ƙudiri a gaban majalisar kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar Ekiti.
Asali: Legit.ng