An Bukaci Tinubu Ya Katse Ziyarar da Yake a Paris Ya Dawo Gida, An Bayyana Dalili

An Bukaci Tinubu Ya Katse Ziyarar da Yake a Paris Ya Dawo Gida, An Bayyana Dalili

  • Wani tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya katse tafiyarsa zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa
  • Omokri ya roƙi Tinubu da ya dawo gida ba tare da ɓata lokaci ba don magance matsalar rashin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta
  • A yayin da ake samun rahotannin hare-hare da dama a wasu garuruwan Najeriya cikin sa'o'i 48 da suka gabata, Shugaba Tinubu na birnin Paris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ado Ekiti, jihar Ekiti - Reno Omokri, tsohon hadimin Goodluck Jonathan, ya ce sace ƴan makaranta da aka yi a jihar Ekiti zai zama wani kyakkyawan dalili da zai sa Shugaba Tinubu ya katse ziyarar da yake a Paris ya dawo Nigeria.

Kara karanta wannan

Duk da 'yarsa na aiki a CBN, sanatan APC ya caccaki mayar da FAAN, CBN zuwa Legas

Omokri, a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Xa ranar Talata, 30 ga watan Janairu, ya ce idan Tinubu ya dawo, "zai nuna hankali" a ɓangaren shugaban ƙasa.

Omokri ya shawarci Tinubu ya dawo gida
Omokri ya shawarci Tinubu ya katse ziyarar da yake yi a Paris Hoto: @DanielBwala, @DavidsOffor
Asali: Twitter

Rashin tsaro: Omokri ya nemi Tinubu ya dawo gida

Shugaban na Najeriya wanda ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa a ranar Laraba 24 ga watan Janairu, 2024 domin wata ziyarar ƙashin kansa, ya shirya dawowa Najeriya a satin farko na watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma Omokri yana son ya dakatar da tafiyar da ya yi zuwa ƙasar waje, duba da cewa ta ƙashin kansa ce, sannan kuma saboda matsalar rashin tsaro a ƙasar nan, musamman a jihar Ekiti.

Omokri ya rubuta a shafinsa X cewa:

"Sace ƴan makaranta da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a jihar Ekiti a safiyar yau, zai zama wani kyakkyawan dalili da zai sa Shugaba Bola Tinubu ya katse tafiyarsa ta ƙashin kansa zuwa Paris ya dawo Najeriya, hakan zai nuna hankali daga ɓangaren shugaban ƙasa, a matsayinsa na uban al'umma, duk wanda ya gaya masa ba haka ba, to ɗan baranda ne wanda ba abokinsa ba ne. Abubuwan sun yi muni."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kisan da aka yi wa sarakunan gargajiya, ya bayar da sabon umarni

Tinubu Ya Magantu Kan Sace Ɗalibai a Ekiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan sace ɗalibai da malamansu da aka yi a jihar Ekiti.

Shugaban ƙasar ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta kuɓutar da mutanen daga hannun waɗanda suka sace su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng