Daga Dawowa Zaman Majalisa, Tinubu Ya Bukaci Ta Amince da Korar Daraktan Wata Hukuma, Ya Nada Wani

Daga Dawowa Zaman Majalisa, Tinubu Ya Bukaci Ta Amince da Korar Daraktan Wata Hukuma, Ya Nada Wani

  • Bayan dawowa zaman Majalisar Dattawa a yau, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin bukata ga Majalisar
  • Tinubu ya bukaci Majalisar ta tabbatar da korar daraktan hukumar FCCPC daga mukaminsa bayan ya kore shi a kwanakin baya
  • Har ila yau, Tinubu ya bukaci Majalisar ta tabbatar da Oluwole Andama a matsayin babban daraktan hukumar kula da albarkatun mai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da korar Babatunde Irukera daga mukaminsa, gidan talabijin na Channels TV ta tattaro.

Shugaban ya bukaci Majalisar ta yi gaggawar tabbatar da korar tsohon shugaban na hukumar FCCPC da ya kora a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Mene ma aka yi, Gwamnan APC ya magantu kan rashin adalcin 'yan Najeriya ga Tinubu, ya ba da tabbaci

Tinubu ya bukaci sahalewar Majalisa kan tabbatar da korar shugaban wata hukuma
Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Amince da Korar Daraktan FCCPC. Hoto: Godswill Akpabio, Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Wasu bukatu Tinubu ya tura Majalisar don amincewarsu?

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da Tinubu ya tura Majalisar wanda shugabanta, Godswill Akpabio ya karanto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya karanto bukatar ce a yau Talata 30 ga watan Janairu yayin zaman Majalisar a Abuja bayan dogon hutu.

Har ila yau, Tinubu ya bukaci Majalisar ta tabbatar da Oluwole Andama a matsayin babban daraktan hukumar kula da albarkatun mai.

Wane mataki Akpabio ya dauka kan bukatun Tinubu?

Akpabio ya mika dukkan bukatun guda biyu ga kwamitocin da suka da ce da bukatun bayan ya karanto su don daukar mataki a kai.

Daga bisani, Majalisar ta shiga tattaunawa don ci gaban kasa wanda ya fi mai da hankali kan tsaro a kasar, kamar yadda ThePledge ta tattaro.

Wannan bukatu na Tinubu na zuwa ne makwanni uku bayan sallamar daraktan hukumar FCCPC kan wasu dalilai.

Kara karanta wannan

An hango Tinubu yana kallon yadda aka rantsar da sabon gwamnan Kogi daga Faransa, hotuna sun bayyana

Har ila yau, a watan Janairun, Tinubu ya kori babban daraktan hukumar BPE, Alexander Okoh tare da maye gurbinsa.

Tinubu zai kara mafi karancin albashi

Kun ji cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya sanya ma'aikatan kasar hawaye kan karin albashi.

Tinubu ya kafa kwamiti don duba yiwuwar karin mafi karancin albashi a kasar da sauran abubuwa da ke cikin dabbaka kudirin.

Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin mai da shugaban ya yi a watan Mayun 2023 jim kadan bayan karbar rantsuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.