Tsohon Kakakin Majalisar Ogun Ya Shiga Babbar Matsala, EFCC Ta Gurfanar da Shi Gaban Kotu
- Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon kakakin majalisar jihar Ogun tare da wasu mutane biyu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abeokuta.
- EFCC na tuhumar Olakunle Oluomo da mutanen biyu da laifin sace naira biliyan biyu da rabi a lokacin da ya ke ofis a 2022
- Sai dai saboda gaza halartar kotun da lauyan EFCC ya yi, Mai shari'a O.O Okere ya dage sauraron karar zuwa 29 ga watan Fabrairu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ogun - An gurfanar da tsohon kakakin majalisar jihar Ogun, Olakunle Oluomo, da wasu mutum biyu a gaban babbar kotun tarayya da ke Oke Mosan, Abeokuta, babban birnin jihar.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Oluomo da mutanen biyu wadanda manyan jami'an majalisar jihar ne bisa zarginsu da karkatar da kudi har naira biliyan biyu da rabi.
An ruwaito cewa sun sace wadannan kudade a lokacin da ya ke rike da mukamin kakakin majalisar a shekarar 2022.
Yan majalisu 18 ne cikin 26 na majalisar suka sa hannu kan a tsige Oluomo bisa zargin jiji da kai, rashin kwarewa, cin zarafin ofis da zargin almundahana, Channels TV ta ruwaito.
Hukuncin da kotu ta fara yanke wa
Sai dai ya garzaya babbar kotun jihar don kalubalantar wannan yunkuri na tsige shi da aka yi.
A ranar Litinin, jum kadan bayan da Oluomo ya gurfana gaban Mai Shari'a O.O Okere, aka gano lauyan hukumar EFCC ba zai samu damar halartar zaman kotun ba.
Da wannan kuma Mai shari'a Okere ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Fabrairu da kuma 1 ga watan Maris.
Wata daliba ta dauki ranta da kanta saboda rabuwa da saurayi
A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda sun ce an kai masu rahoton cewa wata dalibar kwaleji a Adamawa na sha wani abu da ake zargin gubar bera ne ta mutu a gidansu.
Dalibar mai suna Jamima Shetima Balami, ana zargin ta kashe kanta ne biyo bayan furucin saurayinta na cewa ya rabu da ita har abada, lamarin da ya jefa ta a mawuyacin hali.
Balami dai dalibar ND II ce a sashen koyon aikin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Mubi, jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng