Sojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan 'Yan Bindiga Inda Suka Hallaka 30 da Ke Kan Babura a Kaduna
- Rundunar sojin sama ta yi luguden wuta kan wadansu 'yan bindiga a kan babura guda 15 a jihar Kaduna
- Rundunar ta yi nasarar hallaka akalla maharan guda 30 da ke kan babura a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar
- Daraktan yada labarai na rundunar, Edward Gabkwet shi ya bayyana haka inda ya ce maharan sun kai 30
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Rundunar sojin sama ta yi barin wuta kan wadansu 'yan bindiga da ke kan babura 15 a jihar Kaduna.
Rundunar ta yi nasarar hallaka akalla maharan guda 30 a yankin Kwiga-Kampamin Doka da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar.
'Yan bindiga nawa aka kashe a Kaduna?
An shiga dar-dar bayan mahara sun sace 'yan sanda 3 a bakin aiki da ke kare jama'a, bayanai sun fito
Daraktan yada labarai na rundunar, Edward Gabkwet shi ya bayyana haka inda ya ce maharan na kan babura kusan guda 15.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gabkwet ya ce sun samu nasarar hallaka maharan ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan 'yan ta'addan a yankin, cewar Leadership.
Ya ce rahoton ya tabbatar musu da cewa maharan su ne suka kai hari kan rundunar sojoji a Kwanan Mutuwa a ranar 27 ga watan Janairu.
Har ila yau, majiyar ta tabbatar da cewa maharan ne ke kai munanan hare-hare kan farar hula da sace mutane a karamar hukumar.
Ya kara da ce rundunar ta shammace su ne bayan sun taru a wani wuri na musamman don kai hari inda suka farmusu, cewar PRNigeria.
Martanin hafsan sojin saman Nigeriya
Ya ce:
"Bayan zuwan rundunar wurin da ake zargin 'yan bindigan, an tabbatar da cewa su ne a kan babura 15 da ko wane ke dauke da mutum biyu.
"Bayan kai farmakin kan 'yan ta'addan an tabbatar da hallala mafi yawansu dalilin harin."
Hafsan sojin ruwan, Air Marshal Hasan Abubakar ya yabawa rundunar inda ya bukace su da su ci gaba da irin wannan kokari.
An yi garkuwa da 'yan sanda 3
A wani labarin, yayin da rashin tsaro ke kara kamari, an yi garkuwa da wasu jami'an 'yan sanda uku.
Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu a wani kauye a jihar Delta inda maharan suka tafi da bindigogin 'yan sandan.
Asali: Legit.ng