Kebbi: Manoma Za Su Dara Yayin da Gwamna Idris Ya Shirya Ba Su Sabon Tallafi
- Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin samar da man fetur kyauta ga manoman rani a jihar
- Gwamna Nasir Idris ya kuma bayyana cewa tuni ya cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin fara rabon man fetur ɗin ga manoman
- Ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ta kuma raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana don bunƙasa harkokin noma a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kebbi sun kammala shirye-shiryen samar da man fetur ga manoma kyauta.
Gwamnan ya ce za a samar da man fetur ɗin ne ga manoman rani domin bunƙasa noma a jihar, cewar rahoton Daily Trust.
Gwamna Idris ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a mazaɓar tarayya ta Yauri/Shanga/Naski da aka gudanar a ƙaramar hukumar Shanga a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Gwamnatin jihar Kebbi tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya sun kammala shirye-shiryen samar da man fetur ga manoma domin noman rani kyauta."
Manoma za su samu famfunan ruwa a Kebbi
Idris ya kuma ce gwamnatinsa za ta raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana ga manoma 12,000, inda ya ce tuni ta raba guda 6,000.
Bugu da ƙari, gwamnatin jihar za ta sayo famfunan ruwa 20,000 masu amfani da iskar gas, domin ƙara yawan manoman jihar, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Gwamna Idris, yayin da yake karfafa gwiwar manoma da su rubanya ƙoƙarinsu, ya bayyana cewa gudunmawar da suke bayarwa za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin jihar Kebbi ta samu ci gaba da zama jagora wajen samar da abinci.
Gwamnatin Kebbi Ta Gudanar da Auran Gata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta gudanar da bikin aurar da zawarawa da marasa galihu har mutum 300 a jihar.
An gudanr da ɗaurin auren ƴan mata da zawaran ne a fadar Abdullahi Fodio da ke Masarautar Gwandu a Birnin Kebbi a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng