'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Babban Dan Kasuwa a Jihar Arewa
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a jihar Sokoto a wani sabon hari sa suka kai
- Ƴan bindigan sun kai farmaki a garin Tambuwal inda suka yi awon gaba da wani babban ɗan kasuwa mai sayar da kayayyakin gyara
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce tuni jami'anta suka bi sahun miyagun ƴan bindigan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki tashar mota ta Tambuwal da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa a yayin farmakin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da wani mai sayar da kayayyakin gyara.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na yammacin ranar Asabar, 27 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garin Tambuwal nan mahaifar tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, wanda yake riƙe da muƙamin sanata a yanzu.
Ƴan bindigan sun yi harbi cikin iska, wanda hakan ya sanya mutanen wurin suka tsere domin tsira da rayukansu.
Ƴan bindigan sun yi awon gaba da ɗan kasuwa
Sun kai farmaki wani shagon sayar da kayayyakin gyaran motoci inda suka yi awon gaba da mai shagon, Mista Paul Ndibusi Okula.
Sun kuma raunata wani mutum ɗaya wanda a halin yanzu yake karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Wani majiya mai tushe ya bayyana cewa manufar ƴan bindigan ita ce yin garkuwa da mahaifin ɗan kasuwar, wanda ba ya nan a lokacin da suka kai harin.
A cewar majiyar:
"Daga nan sai suka tafi tare da ɗansa mai suna Paul."
Jaridar The Punch ta ce jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, yayin da yake tabbatar da faruwar harin, ya ce ƴan sandan na nan suna bin sahun ƴan bindigan.
Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 10 a yankin Arewa maso Yamma na ƙasar nan.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da alburusai masu tarin yawa a hannun ƴan ta'addan.
Asali: Legit.ng