Manyan Kiristocin Kaduna Sun Waiwayi Sojoji, Sun Rataya Aikin Kare Al’ummarsu a Wuyansu
- Manyan addinin Kirista a Kaduna sun bayyana bukatar sojoji su kare al’ummarsu a yanayin da ake ciki yanzu
- Sun shawarci mazauna Kudancin Kaduna da su rungumi zaman lafiya don ganin ci gaba a yankinsu
- Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da rashin tsaro, musamman a wadannan shekarun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Kaduna - Shugabannin addinin Kirista a Kudancin Kaduna sun daura alhakin kare rayukan mutanensu akan sojojin Najeriya.
Sun kuma yi kira ga jami’an tsaron da su dage wajen tabbatar da ba a ci gaba da kashe Kiristoci mazauna yankin da ma kasa baki daya ba.
Shugabannin a karkashin kungiyarsu ta SCKLA sun kuma bukaci mazauna yankin da su yi watsi da tsohuwar gaba da tashin hankali da ke yankin tare da rungumar zaman lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waye ya yi wannan kira ga sojoji?
Shugaban kungiyar, Emmanuel Nuhu Kure ne ya yi wannan kiran a wani taron addu’a da aka gudanar a Kafanchan ta jihar Kaduna, The Nation ta ruwaito.
Kure ya yi ishara da cewa, mancewa da duk wata kitimurmurar da ta faru a baya tare da fatan samun ci gaba da gina kasa da kawo ci gaba.
A nasa jawabin, Rabaran Israel Akanji, wanda shine shugaban kungiyar gamayyar Kiristocin Baptist ya karfafa gwiwar al’umma da su kasance masu yiwa kasa addu’a.
Ku zauna lafiya don ku ci gaba a rayuwa
Akanji ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masi aikin isar da sakon ubangiji a ko’ina suka tsince kansu, rahoton jaridar Vanguard.
Wakilin Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, Phoebe Yayi ya jaddada bukatar al’ummar da su zauna lafiya don ganin ci gaba a yankinsu.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ake yawan samun rikicin kabilanci da bambancin ra’aui a Arewacin Najeriya.
An yanke mazakutar malamin allo a Zaria
A wani labarin, wani rahoto mai daukar hankali ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke mazakutar wani malamin allo a unguwar Awai da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, matsafan sun yiwa mutumin mai suna Alaramma Salisu Mai Almajirai yankan rago tare da yi masa aika-aikar yanke mazakutarsa a hanyarsa ta dawowa daga karbo kayan cin angoncinsa.
Asali: Legit.ng