“Ku Tuba Ko a Sheke Ku”: Wike Ya Gargadi Masu Garkuwa da Mutane da Masu Yi Masu Leken Asiri
- Miyagu da masu tada kayar baya ba za su ji ta da dadi ba a babban birnin tarayya daga yanzu yayin da Nyesom Wike ya yi sabon barazana
- A wannan karon, Wike ya umurci miyagu da masu kai wa yan bindiga kwarmato akan su mika wuya ko kuma a murkushe su
- Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bukaci mazauna Abuja da su taka muhimmiyar rawar gani ta hanyar taimakawa hukumomin tsaro a yaki da duk wasu nau'i na laifuka a birnin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gargadi masu kai wa yan bindiga kwarmato, masu garkuwa da mutane, masu fashi da makami a babban birnin kasar da su tuba yanzu ko su mutu a jami'an hannun tsaro.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara karfafa kira kan a sauke Wike daga matsayinsa na ministan babban birnin tarayya.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Wike ya yi gargadin ne a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, yayin rufe taronsa na masu ruwa da tsaki a fadin yankunan Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan, wanda ya yi taruka makamancin wannan a Bwari, Gwagwalada, Kwali, AMAC da Abaji, ya rufe shi da Kuje, rahoton Vanguard.
Za mu magance rashin tsaro, Wike
Ministan ya kuma bukaci mazauna kananan hukumomi da su taka rawar ganinsu wajen samar da bayanan da za su taimakawa hukumomin tsaro.
Ya ce:
"Za mu magance rashin tsaro. Wadannan yan fshi da makamin da miyagu, wa'adinsu ya cika. Na san wasu masu yi wa miyagu leken asiri suna nan suna saurarona.
A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa
"Idan kai mai leken asiri ne, za ka mutu ta hanyar da wadannan mutanen da kake kai wa kwarmato za su mutu."
Wike ya fadi masu zuzuta rashin tsaro
A wani labarin kuma, mun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce wasu ƴan siyasa ne ke haddasa tashe-tashen hankula a babban birnin tarayyar ƙasar.
Wike ya yi zargin cewa ana ba masu ɓata sunan na goro don yin farfaganda da kuma tayar da zaune tsaye game da batun sace mutane.
Asali: Legit.ng