Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da Wadanda Suka Sace Shugaban PDP, An Rasa Rai

Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da Wadanda Suka Sace Shugaban PDP, An Rasa Rai

  • A halin da ake ciki, har yanzu shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas yana tsare a hannun yan bindiga, rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da haka
  • A cewar rundunar yan sandar jihar, an ceto mutum tara daga sansanin masu garkuwa da mutane
  • Sai dai kuma, a yayin aikin ceton, wata mata ta rasa ranta yayin da jami'an rundunar yan sandan Najeriya da masu garkuwa da mutane suka yi musayar wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Bilikisu Kazeem, wata mata mai shekaru 37 ta mutu sakamakon harbin da ya same ta yayin da ake musayar wuta tsakanin yan sanda da wadanda suka yi garkuwa da shugaban PDP na Legas a titin Legas-Ibadan.

Kara karanta wannan

Yan sandan Katsina sun aika da dan bindiga barzahu yayin harin da suka kai Dandume

An yi musayar wuta tsakanin yan sanda da wadanda suka sace shugaban PDP a Legas
An Kashe Wata Mata Yayin da Yan Sanda Suka Yi Musayar Wuta da Wadanda Suka Sace Shugaban PDP Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, kakakin rundunar yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ne ya bayyana hakan a Abeokuta, babban birnin jihar.

A cewar Odutola, an ceto mutum tara cikin 10 daga hannun yan bindigar sakamakon musayar wuta da aka yi tsakaninsu da yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi garkuwa da shugaban PDP

Ku tuna an yi garkuwa da Mista Philip Aivoji, shugaban PDP na jihar Legas a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, da misalin karfe 6:00 na yamma a hanyar titin Legas zuwa Ibadan.

Sakataren labaran jam'iyyar a jihar, Hon. Hakeem Amode, ya tabbatar da lamarin.

Sai dai kuma, kakakin yan sandan Odutola, ya bayyana cewa shiga lamarin da jami'an tsaron suka yi ya taimaka wajen sakin tara cikin mutum 10 yayin da shugaban PDP yake tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai yin sojan gona a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar arewa

Da yake magana kan wadanda aka kashe, Odutola ya ce:

“Wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba LSR 288 XE ya lalace, yayin da Eunice Afolake Osalusi, Erinfolami Samuel, Obafemi Da Altantra da Adeyinka Mathew suka ji rauni a kokarinsu na tserewa.
"Raunin ba masu muni bane, suna arfadowa da daidaita a asibiti.
"Abun bakin ciki, wata Bilkisu Kazeem mai shekaru 37 ta rasa ranta kain a isa asibitin. Nan take yan uwanta suka karbi gawarta, inda suka ki amincewa yan sanda su yi mata gwaji."

Kakakin yan sandan ya lissafo kayayyakin da aka samo daga wajen sun hada "bindigar AK47 daya da alburusai 28 wanda ake zargin mallakin bata garin ne, wayoyi, makullin mota, duk an mika su ga masu shi."

Ta kara da cewar mataimakin kwamishinan yan sandan da ke kula da sashin ayyuka ya tattara kwamandoji, inda suka hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da ganin an ceto shugaban na PDP.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki ya sake faruwa a Ibadan yayin da gobara ta tashi a ofishin INEC, an yi karin bayani

Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar ABSU

A wani labarin, mun ji cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami’ar jihar Abia (ABSU) da ke Uturu, (DVC) Farfesa Godwin Emezue.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an sace Emezue ne a wani gidan mai da ke kusa da Amachara, a yankin karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel