Kano: Abba Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kan Abu 1

Kano: Abba Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kan Abu 1

  • Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomin jihar kan sayar da kadarorin gwamnati
  • Gwamnatin ta hannun mataimakin gwamnan jihar ta gargaɗe su da su guji hakan ko su rasa kujerunsu
  • Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama'ar jihar da su kai rahoton duk wanda aka samu yana sayar da kadarorin ba bisa ƙa'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano a ranar Asabar ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 da su daina sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma su rasa kujerunsu.

Mataimakin gwamnan jihar kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi gargaɗin ga shugabannin, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

Gwamnatin Kano ta gargadi ciyamomi
Gwamnatin Kano ta gargadi shugabannin kananan hukumomin jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Gargaɗin ya biyo bayan rahotannin da ke cewa shugabannin na da hannu wajen sayar da kadarorin gwamnati da suka haɗa da gonaki, filaye, shaguna da gidaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu, Dahiru Lawan Kofar Wambai ya fitar, ya gargaɗi shugabannin da su gaggauta dakatar da duk wani siyar da kadarorin gwamnati ba tare da izini ba a yankinsu a faɗin jihar.

Wane gargaɗi gwamnatin ta yi?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mataimakin gwamnan jihar kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayar da wani saƙo mai ƙarfi, inda ya yi gargaɗin cewa gwamnati za ta ɗauki ƙwakƙwaran mataki kan duk wanda aka samu da laifin sayar da kadarorin gwamnati.
"Kwamared Gwarzo ya bayyana cewa an aike da wata tawagar sirri zuwa ƙananan hukumomi daban-daban domin gano tare da damƙe waɗanda ke da hannu wajen sayar da kadarorin gwamnati ba tare da izini ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori wasu hadimai daga aiki a gwamnatinsa, ya naɗa sabbi nan take

"Ya buƙaci jama’a da su ba gwamnati haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk waɗanda aka samu suna sayar da kadarorin gwamnati a faɗin jihar kamar gona, filin kiwo, gidajen gwamnati, rumfunan kasuwa, shaguna da gidaje."

Ganduje Ya Aike da Saƙo Ga Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan yiwuwar dawowar Kwankwaso zuwa APC.

Ganduje ya bayyana cewa da zarar Kwankwaso ya dawo APC to shi ne zai kasance shugabansa a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng