Daga Karbar Rantsuwar Aiki, Sabon Gwamnan Kogi Ya Nada Mambobin Majalisarsa

Daga Karbar Rantsuwar Aiki, Sabon Gwamnan Kogi Ya Nada Mambobin Majalisarsa

  • A ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, ne aka rantsar da Ahmed Usman Ododo a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi
  • Ododo ya sanar da sunayen mambobin majalisarsa yayin da yake jawabi jim kadan bayan daukar rantsuwar aiki
  • Gwamnan ya ce za a mika sunayen mambobin majalisarsa da manyan hadimai gaban majalisar dokokin jihar ba tare da bata lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - A wani lamari da ba a taba ganin irinsa ba, sabon gwamnan jihar Kogi da aka rantsar, Ahmed Usman Ododo, ya zabi yan majalisarsa da wasu manyan mukamai a ranar farko da ya hau mulki.

Ododo, wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, ya gabatar da sunayen wasu kwamishinoninsa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki ya sake faruwa a Ibadan yayin da gobara ta tashi a ofishin INEC, an yi karin bayani

Sabon gwamnan Kogi ya zabi yan majalisarsa
Daga Karbar Rantsuwar Aiki, Sabon Gwamnan Kogi Ya Nada Mambobin Majalisarsa Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

Su wanene suka samu shiga majalisar Ododo?

Sabon gwamnan ya kuma ce za a mika sunayensu gaban majalisar jihar domin ta gaggauta tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa a yayin jawabinsa na karbar rantsuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawancin kwamishinonin da Ododo ya zaba sun kasance mambobin gwamnatin da ta gabata ta Yahaya Bello ne.

Sun hada da tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar, Folashade Ayoade Arike, Kingley Fanwo, Deedat Salami Ozigi, da sauran hadimai, kuma ya bukaci tabbatar da su ba tare da bata lokaci ba.

Wa'adin mulkin Yahaya Bello ya kare a jihar Kogi

Mun dai kawo a baya cewa Gwamna Usman Ahmed Ododo ya karbi ragamar mulkin jihar Kogi, bayan da wa'adin mulkin Yahaya Bello ya kare.

Ana kan gudanar da bukin rantsar da sabon gwamnan a babban filin wasa na Muhammadu Buhari da ke Lokaja, inda Bello ya mika mulki ga Ododo.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Rahotanni sun bayyana cewa dubunnan 'yan jihar ne suka yi tururuwa a filin don gane wa idonsu yadda aka yi bukin rantsuwar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Filato ya magantu kan lamarin tsaro a jihar

A wani labari na daban, mun ji cewa Caleb Mutfwang, gwamnan jihar Plateau, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na taka rawa wajen ƙara taɓarɓarewar matsalar rashin tsaro a jihar.

A makonnin baya-bayan nan dai an kai hare-hare da dama a jihar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen da bai gaza 200 ba, cewar rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng