Ana Fargabar Mutane 30 Sun Mutu Yayin Fada Tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga a Arewa, Bayanai Sun Fito

Ana Fargabar Mutane 30 Sun Mutu Yayin Fada Tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga a Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Kasa da awanni 24 da sassauta dokar hana fita a Plateau, an samu tashin hankali a karamar hukumar Mangu
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a kauyukan karamar hukumar Mangu
  • Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 27 ga watan Janairu a kauyukan Tyop da kuma Satguru a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin fada tsakanin sojoji da mahara a jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 27 ga watan Janairu a kauyuka biyu da ke karamar hukumar Mangu.

An rasa rayuka da dama yayin artabu tsakanin sojoji da bindiga
Mutane 30 Sun Mutu Yayin Fada Tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga a Arewa. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Yawan mutane da suka mutu yayin artabun

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita a karamar hukumar a jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa akalla 'yan bindiga 30 suka mutu yayin da sojoji da dama suka sani raunuka.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da cewa an fara fadan ne da misalin karfe 7:00 zuwa 7:30 a kauyukan Satguru da Tyop, cewar Osun Defender.

An bayyana yadda lamarin ya faru a Mangu

Majiyar ta ce:

"Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 zuwa 7:30 na safe inda 'yan bindigan suka kawo hari a yankin Gindiri.
"An sanar da sojoji inda ba tare da bata lokaci ba sai suka mayar da martani.
"Akalla an kashe 'yan bindiga 30 kuma an kama fiye da 50 yayin da sojoji hudu suka samu raunuka."

Kara karanta wannan

Jirgin Sama dauke da mayan mutane 10 ya yi saukar gaggawa tare da fantsama daji, bayanai sun fito

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'Operation Safe Haven' ya ci tura saboda rashin martaninshi kan lamarin.

Sojoji sun cafke wasu da zargin harin Plateau

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke wasu mutane da zargin su na da hannu a hare-haren jihar Plateau.

Rundunar ta ce ta yi nasarar kama su ne a jiya Juma'a 26 ga watan Janairu yayin wani samame.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai hare-haren kabilanci a karamar hukumar Mangu da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel