Bayan Sarkin Kano Ya Yi Magana, Lauyoyi Musulmai Sun Yi Babban Abu 1 Kan Sace Yaran Arewa Zuwa Kudu
- Bayan Sarkin Kano ya bukaci kawo karshen matsalar satar yara a Arewa, Kungiyar Lauyoyi Musulmai sun bukaci kawo sabon tsari
- Kungiyar ta MULAN ta tabbatar da cewa dole a sake zama don sabunta dokar don hukuncin kisa ko daurin rai rai ga masu laifin
- Shugaban kungiyar a jihar, Barista Sunusi Lawan Fandubu shi ya bayyana haka yayin wani taron ‘yan jaridu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Kungiyar Lauyoyi Musulmai a Najeriya (MULAN) reshen jihar Kano ta yi Allah wadai da garkuwa da kananan yara a jihar.
Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda lamarin ke kara munana a Kano da sauran jihohin Arewacin kasar inda ake daukarsu zuwa Kudancin kasar.
Mene0p MULAN ke cewa kan sace yara a Kano?
Ta kuma ce ba za ta lamunci yadda ake sauya musu addini daga na Musulunci zuwa Kiristanci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar a jihar, Barista Sunusi Lawan Fandubu shi ya bayyana haka yayin wani taron ‘yan jaridu.
Fandubu ya ce ana sace yaran ne don siyar da su ga wasu iyalai don samun saukin ayyukan gida, cewar Daily Trust.
Hadakar da kungiyar ta yi da MURIC
Sunusi ya bukaci a yi gyaran fuska a dokar wacce za ta ba da damar daurin rai da rai ko hukuncin kisa ga wadanda suka aikata laifin.
Ya ce MULAN ta hada kai da Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) don kawo karshen wannan matsala a jihar, cewar Justice Watch News.
Wannan na zuwa ne yayin da sace-sacen yara kanana daga Arewacin Najeriya zuwa Kudanci ke kara kamari.
Lamarin ya yi kamari bayan satar wasu yara da aka yi a Kano da kuma jihar Bauchi da ceto su tare da mika su ga iyalansu.
Sarkin Kano ya yi Allah wadai ta satar yara a Arewa
Kun ji cewa, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi Allah wadai da yadda sace-sacen yara ke kara kamari a Arewacin Najeriya.
Sarkin ya ce dole hukumomi su dauki matakin kawo karshen wannan babban bala’I da ke faruwa a Arewacin kasar.
Asali: Legit.ng