Gwamnan Arewa Ya Sassauta Dokar Zaman Gida Ta Awanni 24 da Ya Sanya a Mangu, Ya Faɗi Dalili 1
- Gwamna Mutfwang na jihar Filato ya sassauta dokar zaman gida da ya ƙaƙaba dare da rana a ƙaramar hukumar Mangu
- A wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar ranar Jumu'a, ya ce a yanzu dokar zata riƙa aiki ne daga 4:00 na yamma zuwa 8:00 na safe
- Celeb Mutfwang ya roƙi mazauna ƙaramar hukumar su bi dokar sau da ƙafa kuma su guji ɗaukar doka a hannunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Filato - Gwamnatin jihar Filato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Celeb Mutfwang, ta sassauta dokar zaman gida ta sa'o'i 24 da ta sanya a karamar hukumar Mangu.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gyang Bere ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a, 26 ga watan Janairu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa
Ya ce a halin yanzu gwamnati ta sassauta wa jama'a, dokar zata riƙa aiki ne daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safiyar kowace rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ingantuwar yanayin tsaro a karamar hukumar Mangu.
An samu ci gaba a yanayin tsaron ne bayan tattaunawa da shugabannin al'umma na addinai da na kabilun yankin karamar hukumar tare da tuntubar majalisar tsaron jihar.
Gwamna ya tura sako ga mazauna Mangu
Gwamna Caleb Mutfwang ya umurci mazauna karamar hukumar Mangu da su kiyaye dokar hana fita da aka sanya a yankin kana su guji daukar doka a hannunsu.
A rahoton PM News, ya kuma buƙaci jami'an tsaro da su tabbatar al'umma na bin dokar kullen sau da ƙafa domin kaucewa yiwuwar sake karya doka da oda.
Mangu ta fuskanci sabbin hare-hare a ranar 23 ga watan Janairu wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30, ciki har da mata da kananan yara.
Lamarin ya tilastawa gwamnatin jihar sanya dokar kulle dare da rana, inda ta buƙaci jami’an tsaro su kamo dukkan masu hannu a aikata wannan ɗanyen aiki.
Wannan rikici ya zo ne makonni bayan jihar ta fuskanci hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Mangu, Bokkos, da Barkin Ladi.
Sojoji sun gano abinda ya haddasa faɗan Mangu
A wani rahoton kuma Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana muhimman abu 2 da suka jawo tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Mangu, jihar Filato.
Kakakin hedkwatar tsaro, Janar Buba, ya ce kisan da wani makiyayi ya yi wa ɗan garin Mangu na cikin abubuwan da suka jawo rikicin.
Asali: Legit.ng