Babbar Nasara: An Kashe Manyan Ƴan Bindiga 3 Yayin Musayar Wuta a Dajin Iyakar Abuja da Kaduna
- Ƴan sanda sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga mai garkuwa da mutane da wasu hatsabibai guda biyu a birnin Abuja
- Kaƙakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a Abuja ranar Jumu'a, 26 ga watan Janairu, 2024
- Yan ta'addan sun baƙuncin lahira ne a hannun dakaru na musamman na IGP da jami'an rundunar ƴan sandan FCT a wani dajin Bwari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Dakarun ƴan sanda na tawaga ta musamman da jami'an rundunar ƴan sandan Abuja sun yi nasarar halaka manyan ƴan bindiga 3 a dajin da ke Bwari, Abuja.
The Nation ta ce ƴan sandan sun sheƙe ƴan bindigar ne da sanyin safiyar yau Jumu'a, 26 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 2:00 na dare a wani daji da ya haɗa Abuja da Kaduna.
Daga cikin ƴan bindigan da suka sheƙa barzahu harda wani hatsabibin mai garkuwa da mutane kuma shugaban tawaga, Mai Gemu, wanda aka fi sani da Godara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Godara tare da ƴan tawagarsa sun jima suna kai hare-haren kan mazauna babban birnin tarayya da maƙotan jihohi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a yayin nuna mutum 20 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Yan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga
Adejobi ya ce jami'an tsaron sun yi artabu da tawagar ƴan bindigar a dajin, inda suka kashe uku daga cikinsu kuma Magamu, shugaban ƴan bindigar na cikin waɗanda aka kashe.
A rahoton Daily Trust, kakakin ƴan sandan ya ce:
"Da sanyin safiyar yau Juma’a, jami’an DFI-IRT suka yi artabu da wasu ‘yan bindiga a yankin, inda suka kashe 3 daga cikinsu ciki har da shugaban tawagar mai suna Mai Gemu Godara.
"Zamu iya faɗa da izza cewa an tarwatsa sansanin waɗannan ƴan ta'adda, daga yau duk wata tawagar masu garkuwa a Bwari da iyakokin Kaduna sun yi sallama da zaman lafiya domin ba zamu barsu ba."
Masu garkuwa sun nemi fansa N200m
A wani rahoton kuma Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da shugaban PDP na jihar Legas da wasu jiga-jigai sun nemi N200m a matsayin kuɗin fansa.
Mista Philip Aivoji da wasu mambobin PDP na hanyar dawowa daga Ibadan ranar Alhamis lokacin da ƴan bindiga suka sace su.
Asali: Legit.ng