Jirgin Sama Dauke da Mayan Mutane 10 Ya Yi Saukar Gaggawa Tare da Fantsama Daji, Bayanai Sun Fito
- An shiga yanayin dar-dar bayan wani jirgin sama dauke da manyan mutane masu alfarma ya yi saukar gaggawa a Oyo
- Jirgin na dauke ne da mutanen guda 10 inda ya fantsama cikin daji a kokarin sauka a filin jirgin sama da ke Samuel Ladoke Akintola
- Lamarin ya faru ne a yau Juma'a 26 ga watan Janairu a Ibadan da ke jihar Oyo da misalin karfe 11 na rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - An shiga tashin hankali bayan jirgin sama ya yi saukar gaggawa a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.
Jirgin wanda ke dauke da manyan mutane guda 10 ya yi saukar gaggawar ce tare da fantsama cikin daji.
A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa
Yaue lamarin ya faru a Ibadan?
Channels TV ta tattaro cewa jirgin ya samu matsalar a yau Juma'a 26 ga watan Janairu da misalin karfe 11 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin wanda ya faru a a filin tashi da saukar jirage na Samuel Ladoke Akintola a jihar ya ta da hankulan jama'a.
Hukumar kashe gobara daga Ma'aikatar kula da jiragen sama ta yi gaggawar isa wurin don ba da agaji.
Sai dai ba a samu rasa rai da munanan raunuka ba yayin dirar gaggawar da jirgin ya yi a Ibadan.
Martanin hukumomin NCAA da NSIB
Kakakin hukumar NSIB, Tunji Oketunmbi ya tabbatar da faruwar lamarin bayan tuntubarshi da 'yan jaridu suka yi.
Yayin da kakakin hukumar NCAA, Carol Adekotujo ya tabbatar da cewa ba a samu rasa rai ba yayin hatsarin, cewar Vanguard.
Ya ce:
"Jirgin sama ne mai zaman kansa daga Abuja, ya sauka lafiya sai dai yanayin firgici inda ya kauce wa hanya, babu rasa rai."
Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a Abuja
Kun ji cewa wani Jirgin sama mallakin kamfanin Aero Contractors ya gamu matsala a sararin samaniya wanda ya tilasta masa juyo wa cikin gaggawa.
Wani fasinjan jirgin da lamarin ya shafa ya ce Jirgin saman ya yunkura ya tashi zuwa sararin samaniya da misalin karfe 8:40 na safe.
Asali: Legit.ng