Murna Bayan Sojoji Sun Cafke Wasu da Zargin Kai Harin Plateau, an Samu Abubuwa Tare da Su
- Rundunar Operation Safe Haven' ta tabbatar da cafke wasu mutane da ake zargi da kai harin Mangu a Plateau
- Rundunar ta ce ta yi nasarar cafke mutanen da kuma muggan makamai a tare da su da suke amfani da su wurin kai harin
- Hausa Legit ta ji martanin wasu mazauna garin Jos kan hare-haren da ake kai wa yankin Mangu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Rundunar sojin 'Operation Safe Haven' ta yi nasarar cafke wasu kan zargin kai harin Mangu a jihar Plateau.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun kisa kai hare-haren ne duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya a karamar hukumar.
A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa
Me ake zargin wadanda aka kaman?
Har ila yau, rundunar ta kwato muggan makamai a hannun wandanda ake zargin da suka yi amfani da su a harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta bayyana haka ta bakin jami'in yada labaran 'Operation Safe Haven', Oya James ya fitar a yau Juma'a 26 ga watan Janairu a shafin X.
Sanarwar ta ce:
"Rundunar 'Operation Safe Haven' ta na Allah wadai da harin matasan Kerang da kuma lalata dukiyoyin al'umma.
"Bayan lalata dukiyoyi da barna, sun kuma farmaki rundunar sojin sama da ke tabbatar da dokar hana fita a yankin."
Makaman da aka samu a wurinsu
Sanarwar ta kara da cewa:
"Rundunarmu ta yi nasarar cafke wadanda suka kai harin tare da kwato muggan makamai a tare da su."
Daga cikin makaman akwai bindiga kirar Ak-47 da bindugu guda hudu da bam kirar hannu, cewar The Nation.
Sauran sun hada da karamar bindiga korar 'Pistol' da 'Boris' guda 36 da alburusai masu tarin yawa.
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna garin Jos kan hare-haren Mangu da kuma nasarar cafke wasu.
Aliyu Mohammed ya ce tabbas wannan kama matasan da aka yi abin murna ne fatan dai kawai a tabbatar an hukunta su dai dai da laifinsu.
Musa Dan Jos ya ce:
"Babban damuwarmu shi ne gwamnati ta kawo karshen tashin hankali a Plateau maganan kama wasu duk ba shi ba ne."
Dan Jos ya kara da cewa sau da yawa an sha kama irin wadannan amma daga baya sai ka rasa ina aka yi da su.
Rundunar soji ta musanta hannu a harin Plateau
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi martani kan zargin hannunta a cikin hare-haren jihar Plateau.
Rundunar ta musanta zargin inda ta ce jami'anta ba sa nuna bangaranci yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban CAN a Mangu ya zargi sojojin da hannu a kisan Kiristoci.
Asali: Legit.ng