Kasar China za ta ba ‘Daliban ABU Zariya gudumuwar karatu

Kasar China za ta ba ‘Daliban ABU Zariya gudumuwar karatu

- Kasar China ta zabi ‘Dalibai masu kwazo daga Jami’ar ABU

- Za a ba wadannan ‘Dalibai gudumuwar karatu a kasar ta Sin

- Shugaban Jami’ar Farfesa Garba yace ABU tayi nisa a Nahiyar

Kasar China ta zakulo wasu gwarazan Daliban da su ka yi karatu a fittaciyyar Jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Garin Zariya har su 47 inda ta shirya ba su taimakon karatu a kasar. Daliban su na da makin awo na CGPA da ya haura 4.68.

Kasar China za ta ba ‘Daliban ABU Zariya gudumuwar karatu
China za ta ba wasu 'Daliban Najeriya horo

Gwamnatin Kasar China ta yabawa yunkurin da Jami’ar ta ABU tayi na hada-kai da ita wajen ba ‘Daliban ta gudumuwa don haka ne aka zabi ‘Daliban da su ka gama Digiri da mataki na farko domin su amfana daga kasar da ke Nahiyar ta Asiya.

KU KARANTA: Gobara tayi wa 'Yan kasuwa barna a Jihar Kano

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, Shugaban Jami’ar Ibrahim Garba ya bayyana cewa Jakadan Najeriya zuwa kasar ta Sin watau China Dr. Zhou Pingjian ne yayi wa wadannan ‘Daliban kokari a dalilin alakar da ke tsakanin manyan kasashen.

Akwai dai kawance mai kyau tsakanin Najeriya da kasar Sin wanda kowane ya samu ‘yanci a Ranar 1 ga Watan Oktoba amma ba a shekara guda ba. Najeriya ce dai babbar kasa a Nahiyar kamar yadda Kasar ta China ta ke babba a Nahiyar ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng