Kano: Kotu Ta Dauki Mummunan Mataki Kan ’Yan Bijilanti 5 Saboda Dalili 1 Tak, Sun Yi Martani

Kano: Kotu Ta Dauki Mummunan Mataki Kan ’Yan Bijilanti 5 Saboda Dalili 1 Tak, Sun Yi Martani

  • Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yi hukunci kan wasu matasa 'ya bijilanti guda biyar a jihar
  • Matasan da aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ana zarginsu da kisan wani matashi a jihar
  • Mai Shari'a, Dije Audu Aboki wacce ta jagoranci shari'ar ta bayyana hukuncin a yau Alhamis 25 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yanke hukuncin rataya kan wasu 'yan bigilanti guda biyar.

Ana zargin matasan da kisan wani matashi dan shekaru 17 mai suna Ahmed Musa, cewar Tribune.

Kotu ta yi hukunci kan wasu matasa 5 a Kano
Kotu Ta Dauki Mataki Kan ’Yan Bijilanti 5 Kan Zargin Kisan Kai a Kano. Hoto: High Court.
Asali: UGC

Wane mataki kotun ta dauka kan matasan?

Kara karanta wannan

Kisan Ummita: Kotu ta tsayar da ranar da dan China zai san makomarsa

Wadanda ake zargin sun hada Mustapha Haladu da Emmanuel Korau da Auwal Ja'afar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran matasan biyu da ake zargi da kisan sun hada da Irimiya Timothy da kuma Elisha Ayuba, cewar Platform Times.

Mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun 2022.

Har ila yau, sun aikata laifin ne a Sabon Titi da ke Panshekara a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar, cewar Punch.

Yadda matasan suka yi ajalin Musa

Lamido ya fada wa kotun cewa matasan sun yi ta dukan matashin da katako inda marigayin ya rike katakon da suke dukansa da shi.

Har ila yau, daya daga cikinsu ya ciro wuka inda ya caka matashin a wuya tare da daukarsa a cikin adaidaita sahu.

Kara karanta wannan

Rikici Tsakanin Boko Haram Da ISWAP Ya Yi Ƙamari Yayin Da Suka Kashe Juna a Sabon Rikici

Ya ce daga bisani an dauki matashin zuwa ofishin 'yan sanda na Kuntau da kuma asibitin Murtala inda aka tabbatar ya mutu.

Bayan karanto musu dukkan zarge-zargen da ake yi, matasan sun musanta aikata kisan.

A karshe, Mai Shari'a ta yabawa Soron Dinki wurin gabatar da shaidu da hujjoji kan shari'ar inda ta ce ta amince da dukkan abin da ya gabatar.

Ta ce:

"Na yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga matasan guda biyar da ake zargi."

Kotu ta yi hukunci kan matsalar Majalisar Plateau

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan shari'ar Majalisar jihar Plateau.

Kotun ta ce ba za ta dakatar da kakakin Majalisar daga amincewa da sabbin 'yan Majalisun APC 16 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.