Fayose Ya Fusata Yayin da Ya Tsare Wani Minista Kan Karya Dokar Tuki, Bidiyon Ya Yadu

Fayose Ya Fusata Yayin da Ya Tsare Wani Minista Kan Karya Dokar Tuki, Bidiyon Ya Yadu

  • Isaac, kanin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana yadda ya dakatar da motar wani minista da ke kokarin take dokar tuki a titi
  • Fayose ya yi bayanin cewa lamarin ya afku ne a yankin Maitama da ke Abuja, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda babu wanda ya fi karfin doka
  • An gano kanin tsohon gwamnan yana kira ga wani wani DPO a kan ya mayar da ministan baya, amma ya ki bayyana kowani minista ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Isaac, kanin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce ya tsayar da motar wani minista wanda ya saba dokar tuki a titi a yankin Maitama da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da Hisbah ke kokarin kama Murja, Sheikh Rijiyar Lemo ya yi magana kan ayyukan hukumar

Fayose ya tsare minista kan take dokar tuki
Fayose Ya Fusata Yayin da Wani Minista Ya Karya Dokar Tuki a Titi, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Prince Isaac Fayose
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, matashin ya rubuta:

"Sai da na tsayar da wani minista a yau kan bin hanyar da bai kamata ba a Maitama Abuja...Babu wanda ya fi karfin doka...Nagode, ya mai girma minista, da ka rike mutuncinka."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, an jiyo kanin tsohon gwamnan yana bukatar wani dan sanda a kan ya mayar da ministan baya domin ya je ya bi hanyar da ta dace.

Isaac Fayose ya hana minista take dokar tuki

Ya fada ma DPO din cewa:

"Ka mayar da su baya kan bin hanya daya, ku goma, ku ba hukuma bane, ba hukuma bane su. Ka kora su baya yanzun nan."

Fayose ya ci gaba da cewa:

"DPO, sunana Isaac; ya zama dole a tsare yaron nan. Ka koma baya. Idan kai minista ne, shin kasar da muke muradi kenan? DPO na magana da kai. Ka koma yanzu, ka shiga motarka sannan ka koma baya."

Kara karanta wannan

"Ba zai illata arewa ba": Jigon PDP ya magantu kan mayar da manyan ofisoshi Legas

Sai dai kuma, bai bayyana sunan ministan da ake magana a kansa ba.

Fayose dai ya yi gwamna sau biyu a jihar Ekiti karkashin inuwar jam'iyyar PDP. An ji shi sosai a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

Kalli bidiyon a kasa:

Shehu Sani ya karyata batun mayar da FCT Legas

A wani labari na daban, mun ji cewa ana tsaka da rade-radin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin dauke babban birnin tarayya daga Abuja zuwa Legas, Sanata Shehu Sani ya bayyana hgakan a matsayin babban aiki ja.

A cewar tsohon dan majalisar tarayyar, yin haka yana bukatar bin matakai na kudin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng