Budurwa Ta Yi Murnar Shafe Shekaru 5 Ba Tare da Namiji Ya Kusanceta Ba, Mutane Sun Yi Martani

Budurwa Ta Yi Murnar Shafe Shekaru 5 Ba Tare da Namiji Ya Kusanceta Ba, Mutane Sun Yi Martani

  • Wata matashiyar budurwa ta bayyana cewa shekarunta 35 a duniya kuma tsawon shekaru biyar kenan bata yimu'amalar kwanciya da 'da namiji ba
  • Kame kai daga 'da namiji wani mataki ne da mutum kan dauka saboda al'ada ko kuma wasu dalilai na gashin kai, kuma yana da amfani
  • Jama'a sun yi martani kan wannan lamari, inda mutane da dama suka bayyana tsawon lokacin da suka shafe suna kame kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mutane kan dauki matakin tsarkake kansu daga 'da namiji saboda dalilai daban-daban. A bangaren wasu ya kan kasance saboda al'ada yayin da wasu ke ganin hakan na taimakawa lafiyar kwakwalwa.

Matashiya ta tsarkake kanta
Budurwa Ta Yi Murnar Cika Shekaru 5 Ba Tare da Namiji Ya Kusanceta Ba, Mutane Sun Yi Martani Hoto: @ntombi_nkosi
Asali: UGC

Budurwa ta yi murnar tsarkake kai na tsawon shekaru biyar

Wata yar TikTok, @ntombi_nkosi, tana cikin mutanen da suka yanke shawarar tsarkake kansu daga 'da namiji.

Kara karanta wannan

“Wannan ramar ba ta maki kyau ba” Sabon hoton Hadiza Gabon ya haddasa cece-kuce

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tana cikin shekaru biyar kenan rabonta da yin mu'amalar kwanciya da 'da namiji, kan haka ne ta saki bidiyo tana mai farin ciki da taka rawa yayin da take sanar da duniya wannan ci gaban.

Kalli bidiyon tsarkakkiyar matar a kasa:

Yan TikTok sun ba da labarin tsarkakewarsu

Bidiyon ya samu 'likes' 6,000, sannan mutane da dama sun bada labarin tsawon lokacin da suka shafe suna tsarkake kansu.

@Zamachi Mpaxa ta ce:

"Abu ne mai yiwuwa amma sai mutum ya dage da farko kana bukatar yanke shawara sannan ka tsaya kan haka."

@Asa ta yi martani"

"Watanni shida kuma gani da karfina...Abun mamaki ne yadda mutum baya ma jinsa zuwa wani lokaci."

@What country? :

"Ina tayaki murna."

@Katli babe:

"Shekara 1 da wata 1 kuma ina ci gaba na jajircewa ina tayaki murna masoyiyata kuma barka da zagayowar ranar haihuwa."

Kara karanta wannan

Bidiyon gawurtaccen shugaban yan bindiga mai karbar haraji a kauyukanZamfara bayan an kama shi

Matashiya ta baje kolin nasarorinta

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya ta fito ta sanar da mabiyanta na soshiyal midiya tarin nasarorin da ta samu a rayuwa.

A wani bidiyo da @fumy_layor ta wallafa, matashiyar ta bayyana karara cewa ta cimma abubuwa masu tarin yawa a shekaru 24 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng