Bidiyon Gawurtaccen Shugaban Yan Bindiga Mai Karbar Haraji a Kauyukan Zamfara Bayan An Kama Shi
- Al'ummar jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya za su samu sauki bayan kama gawurtaccen shugaban yan bindiga da ya addabe su
- Kamar yadda aka bayyana a wani bidiyo da ya yadu, shugaban yan bindigar ya shahara sosai wajen kakabawa mazauna yankin biyan haraji da cinsu tara
- Ya'u Babban Kauye ya yi bayani filla-filla kan irin kudaden da ya dungi karba daga al'ummar wasu kauyuka a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Jami'an rundunar tsaro sun yi nasarar kama wani gawurtaccen dan bindiga mai suna Ya'u Babban Kauye da ya addabi al'ummar Zamfara.
Ya'u Babban Kauye ya kasance shugaban yan bindiga wanda ya yi kaurin suna wajen kakabawa al'umman yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara haraji.
Dan ta'addan yana cin tarar al'ummar kauyukan da ke wannan yanki, tare da yin barazanar kawo mayakansa domin su ci da duk wadanda suka ki biyan harajin da yaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai amfani da shafin X, @ZagazOlaMakama, ne ya wallafa bidiyon dan ta'addan da aka kama a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
Da yake bayani a cikin bidiyon, dan ta'addan ya yi bayani dalla-dalla na yawan kudaden da ya karba daga wajen al'umma, da kuma mutanen da ya kashe.
Ya kuma bayyana cewa ya mallaki bindigar AK 47 wanda ya siya, sannan ya ce akwai wasu karin bindigogi biyu da suke ta'asar tasu da su amma mallakin wani yaronsa ne.
Har ila yau, Ya'u ya karbi bakin kashe wani jami'in dan sanda wanda ya harzuka shi sakamakon kashedin da ya yi masa kan kada ya kara sanya hular yan sanda da ya gani a kansa.
"An yi masa mugun duka": Shehu Sani ya yi martani yayin da shugaban makarantar Kaduna ya shaki yanci
Da aka tambaye shi kan dalilinsa na kashe jami'in dan sandan alhalin bai yi masa komai ba, Ya'u ya ce kaddara ce ta kai shi ga aikata hakan.
Su wanene suka kama Ya'u Babban Kauye?
Sai dai kuma, har yanzu rundunar yan sandan jihar Zamfara bata fitar da wata sanarwa a kan haka ba.
Legit Hausa bata tabbatar da ko rundunar yan sanda ko na soji bane suka kama dan ta'addan.
Ministan Tinubu ya koka kan barazana da rayuwarsa
A wani labarin, ministan harkokin ma’adanan kasa, Dele Alake ya tabbatar da cewa yana fuskantar barazana saboda kalaman da ya yi.
Kwanan nan aka ji Mai girma Ministan ya fito yana zargin manya da hannu wajen hura wutar ta’addanci, Legit ta fitar da rahoton nan
Asali: Legit.ng