Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Shugabanta
- An tsige Pa Ayo Adebanjo, mukaddashin shugaban kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere daga kan kujerarsa
- Afenifere ta tsige Adebanjo a matsayin shugabanta a taronta na wata wanda ya gudana a gidan Pa Reuben Fasoranti,jagoran kungiyar, a Akure, babban birnin jihar Ondo
- Hakan na zuwa ne watanni bayan takaddamar da ta biyo bayan dan takarar da Adebanjo ya marawa baya sama da zabin mutane da yawa a kungiyar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Akure, Ondo - Kungiyar dattawan Yarbawa ta Afenifere ta tsige Ayo Adebanjo a matsayin mukaddashin shugaban kungiyar.
An tsige Adebanjo ne a wajen taron wata na kungiyar wanda ya gudana a gidan jagoranta, Reuben Fasoranti, a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Yadda aka tsige Adebanjo a matsayin shugaban Afenifere
Kamar yadda TVC ta rahoto, wani Farfesan tiyata Samuel Ibikunle mai ritaya ne ya gabatar da kudiri a kan haka, kuma Agboluaje daga jihar Oyo ya goyi bayansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan shawarar da dattawan kungiyar ta Afenifere suka bayar.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a karshen taron, kakakin kungiyar ta Afenifere, Jare Ajayi, ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai da kuma magance rabuwa.
Ku tuna cewa alaka ta yi tsami tsakanin Adebanjo da Fasoranti, lamarin da ya sa shi fitowa ya yi bayanin cewa an nada tsohon shugaban jam'iyyar ne don ya yi riko a madadinsa saboda tsufa.
Yadda Adebanjo ya raba gari da Fasoranti a Afenifere
Rabuwar kan ya fara ne lokacin da Adebanjo ya lamuncewa Peter Obi, dan takarar jam'iyyar LP gabannin zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
A daya bangaren, tsagin Fasoranti sun lamuncewa Shugaban kasa Bola Tinubu, wanda shine dan takarar APC a zaben.
Tsagin Fasoranti ya yi bayanin cewa makasudin gina kungiyar shine daraja Bayarabe sama da komai. Don haka, suka ga ya cancanci su marawa Tinubu, Bayarabe baya, a matsayin dan takararta a zaben.
Rigingimun sun ci gaba har bayan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, kuma Tinubu ne ya lashe zaben.
FG ta karyata mayar da Legas babban birnin Najeriya
A wani labarin, Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin labarai ya yi watsi da rade-radin cewa Shugaban kasar na son mayar da babban birnin tarayyar kasar zuwa Legas.
Onanuga ya ce rade-radin mayar da babban birnin tarayyar kasar Legas ya fara ne a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 daga bangaren abokan hamayyar Tinubu.
Asali: Legit.ng